Saturday 14 October 2017

Nishadi: TATSUNIYAR SARKI MAHLANU DA 'YAN MATA

Tura Wannan Zuwa
(wannan tatsuniya ce tsohuwa wadda aka
samota daga al'ummar Bantu dake nan Afirka.)


Marubuci: SADIQ TUKUR GWARZO

A wani lokaci mai tsawo daya gabata, anyi wani
mutum wanda yake da 'ya'ya biyu. Dukkan su
yan mata ne, kuma sun isa aure.

Rannan sai wannan mutum ya tsallaka ruwa
izuwa wani gari domin ziyara. Da isar sa sai yake
jin labarin sarkin Garin wanda hamshaki ne yana
neman aure, kuma an gwada dukkan yan matan
garin amma basuyi masa ba.

Dawowar sa gida keda wuya sai ya sanar da
iyalinsa. Babbar 'yarsa wadda sunan ta
Mpunzikazi, tace zata je domin auren sarki.
Mahaifinta yayi murna da haka, ya turawa yan
uwa da abokansa na arziki don suzo a rakata
izuwa garin ta yadda zata zamo matar sarki,
amma sai mpunzikazi tace tafi son a barta taje
ita kadai.
Washe gari taci kwalliya ta kama hanya, tana
cikin tafiya sai ta hadu da Bera. Bera ya matso
gareta yace "kina so na nuna miki hanya?''. Sai
kuwa mpunzikazi tayi tsaki, tace "gafara nan,
waye kai da zaka nuna min hanya?"
Daga nan
bata kara bi takansa ba ta wuce.
Shikuwa sai
cewa yayi "indai a haka zaki to bazaki ci nasara
ba".
Tayi gaba kenan, sai ga kwado yazo gareta.
Kwado yace "idan kinaso zan nuna miki hanya".
Sai kuwa ta daka masa tsawa, tace "kai kauce,
har ka isa kayi magana da matar sarki?"
Sai kwado yace kije gaba, zakiga abinda zai faru"
Taci gaba da tafiya kenan sai ga wani yaro yana
kiwon dabbobi.

Da ganinta sai ya matso kusa
yana cewa "yayata ina zuwa haka?"
Mpunzikazi taja tsaki tace " waye kai da zaka
kira ni da yayarka? Kai kauce kabani wuri."
Yaro ya kara cewa "ina jin yunwa, ko zaki
taimakeni da abinda zanci?"
Sai kuwa ta kara daka masa tsawa tace " ka
kauce ka bani wuri fa nace!!!"
Sai yaro yace " ai kuwa indai haka zakiyo, to ba
zaki dawo ba"
Mpunzikazi dai ta wuce gaba.
Tayi gaba kenan,
sai ga wata tsohuwa tana zaune bisa wani
dandamalin dutse.
Tsohuwa tace "sannu da zuwa
'yar nan ga shawara zam baki: idan kika je gaba
zaki ga bishiyoyi suna miki dariya, kada ki sake
kiyi musu dariya.

Zaki ga kabakin madara da
zuma, kada ki sake kisha, sannan zakiga wani
mutum wuyansa a saman kansa, yana dauke da
ruwan sha, ko yayi miki tayi kada kisha".
Sai kuwa Mpunikazi tayi tsaki tace " wannan
mummunar tsohuwa da rigima take, ko meye
ruwanta dani oho?"
Ai kuwa wucewar ta keda wuya, sai ga bishiyoyi
na dariya, nan itama ta kyalkyale musu da dariya.
Taga kuttun zuma da madara, ta zauna ta
sharba, taga mutumin da wuyansa ke saman
kansa ya bata ruwa ta karbe tasha.
Bayan duk an gama wannan ne ta iso kofar
garin.
Zata shiga kenan sai ga wata budurwa
zata debo ruwa, ashe yar uwar sarkin ce.
Budurwar tace da mpunzikazi "yar uwata ina
zakije ne haka?"
Mpunzikazi tace " wacece ke da kike min
wannan tambayar? To nice matar da sarkin ku
zai aura"
Sai budurwar tazo gare ta tana cewa "tsaya na
nuna miki ta hanyar da zaki shiga garin" Amma
ina, mpunzikazi bata kula taba, ta wuce kurum
abinta.
Da shigarta garin sai mutanen garin suka
tambayeta abinda a kawota, ita kuma ta fada
musu, sai akace mata sarki baya gari yanzu,
amma ga hatsi ta girka masa abinci, idan ya
dawo zaici.
Haka kuwa akayi. Bayan ta gama abinci zuwa
yamma, sai ga guguwa na kadawa, alamun sarki
ya dawo kenan.
Zuwa can aka ce tazo sarki zai ganta. Da
shigarta inda sarkin yake sai ta tsorata, domin
kuwa wani katon maciji ta gani mai kawuna
biyar, a yaren su ana kiransa 'Makanda Mahlanu'.
Ta ajiye masa abincin data girka yaci, sai kuwa
yace abincin ba dadi don haka bata cancanci
zama matar sa ba, nan take ya kanannadeta ya
kashe ta.

Labari sai yazowa yan uwanta cewa batayi
nasara ba.
Hakan yasa kanwarta shirin cewa
itama zata jarraba. Sunan ta mpunzanyana.
Ubanta yace zai tara mutane suyi mata rakiya,
tace to baba babu matsala. Da ranar tafiya tazo
sai suka fita suka kama hanya. Can sai ga bera a
gaban su. Bera yace "yarinya ko kina so na nuna
miki hanya?"
Mpunzanyana tace "ai kuwa zanji dadi idan ka
nuna min ta inda zamu bi". Daga nan sai ya nuna
musu inda zasu bi, suka wuce.
Sunyi gaba kenan sai ga wata tsohuwa. Tsohuwa
tace "yarinya bari na baki shawara, idan kika yi
gaba zakiga hanya ya kasu biyu, babba da
karama, to karamar zaki bi"
Mpunzanyana tace
"Nagode babata, zanyi kamar yadda kika ce"
Haka kuwa akayi kamar yadda tsohuwa ta fada,
suka bi karamar hanya.

Daga nan kuma sai ga
kwado. Kwado yace " bari na baki shawara, idan
kika je garin zakiga wata budurwa a bakin kofa,
ki girmamata yar uwar sarki ce, za kuma ace kiyi
ma sarkin abinci, ki tabbata kinyi abinci mai dadi,
sannan idan kika ga sarkin kada ki tsorata"
Mpunzayana tayi godiya ta wuce.
Bayan sun isa kofar gari, sai ga budurwa yar
uwar sarki. Ta tambaye su abinda ya kawo su,
mpunzayana ta fada mata, sai kuwa budurwar ta
nuna musu ta hanyar da ya kamata su shiga
garin.

Shigar su keda wuya aka gabatar musu da hatsi
domin tayiwa sarki abinci kafin dawowar sa.
Mpunzayana ta natsu tayi girki mai kayatarwa.
Zuwa yamma sai taji guguwa na tasowa, alamun
sarki ya dawo kenan.

Ta dauki abinci ta nufi inda akace mata yake.
Ta
ganshi katon macici mai kawuna biyar, amma ta
dake ba tare da taji tsoro ba, ta gabatar masa da
abincin. Da macijin yaci abincin sai yaji dadin sa,
yace hakika itace matar dazai aura.
Kawai sai
taga yayi birgima ya rikide izuwa santalelen
saurayi.

Akayi biki gagarumi, ya sanyata a gidan sarauta
tare da duk yan uwanta. Ya zama yana matukar
kaunar ta.
Shikenan, kurunkus..

**Darasin Tatauniyar shine; Tarbiyya.
Hakika
babu mai iya cin nasara a rayuwa matukar yana
kaskanta nutane, baya girmama su.

Allah ya bamu dacewa amin.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishadi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHADANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com 

Za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode


TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user