Saturday 14 October 2017

ALLAHU AKBAR: TARIHIN DAN KASUWA ALH MUHAMMADU DANGOTE

Tura Wannan Zuwa

Daga littafin Kano cibiyar Kasuwanci ta afirka
wanda Marigayi Maje Ahmad Gwangwazo Allah
yajiqansa ya wallafa.

Shine Muhammadu ɗangote ɗan Mallam Ali ɗan
Shekarau, bafullatani mutumin kasar Kura ta jihar
kano.

An haife shi a wani gari mai suna Gwate dake
kasar Nijar, a sanda Mahaifansa suka je garin
domin fatauci a shekarar 1903 abar tunawa,
wadda turawa suka zo Kano.

Bayan haihuwar sane sai mahaifansa suka komo
garinsu Kura da zama, acan ne kuma ya taso
tare da samun ilimin addini. Ance Babban
Malaminsa sunansa Malam Ami, makarantarsa
nanan a unguwar Tukuba layin Alhaji Ibrahim Mai
karofi.

Bayan da Allah yayiwa mahaifiyarsa mai suna
Hadiza rasuwa, sai kakarsa mai suna Rabi ta
nemi ya dawo hannunta da zama, ita kuma ta
kasance tana zaune a cikin birnin kano ne.

Hakan
kuwa akayi, domin mahaifinsa ya aminta da haka,
inda ya dawo unguwar Makafin Dala ta birnin
kano da zama, anan kuma ya sauke littafin
Alkurani maigirma, a hannun malaminsa mai suna
Mallam Abubakar.

Daga bisani kuma sai kakar sa ta bashi jalin kuɗi
Sulai biyar domin ya soma taɓa kasuwanci dasu.

Ance Alhaji Muhammadu ɗangwate ya soma ne
da siyar da yadiddika anan unguwar
Kududdufawa, sannan ya koma cinikin kwanika a
'yanmota ta kasuwar kantin kwari inda yakan siyi
kaya daga hannun kamfanonin turawa irinsu
johnholt, GBO, UAC da kamfanin PZ na kasar
faransa.

Sannu a hankali sai Alhaji Muhammadu
Dangwate ya shiga harkar siyasa, inda ya shiga
jamiyyar N.P.C har kuma ya tsaya takarar ɗan
majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar
kura.

Ance ya samu nasarar wannan zaɓe, inda
suka shafe shekaru uku suna wakilci mai amfani
ga alummarsu, watau daga shekarar 1963-1966.

Waɗanda suka rayu dashi, sun bayyana shi a
matsayin mutum nagartacce wanda baya kin
talaka, mai hakuri, mai taimakon nakasa gami da
son abokai kuma.

Sannn ance yayi mu'amala da manyan mutane ta
fannin siyasa da sarauta na lokacinsa.

Ance babban abin koyi a rayuwarsa shine tashi
tsaye domin neman na-kai, kyauta tare da
taimakon al'umma.

Shine akace akwai wata rana sanda aka haifi
Marigayi General Sani Abacha, kasancewar
Attajiri Alhaji Abacha amininsa ne, ya halarci
wurin raɗin sunan amma a makare. To anan ne
wani maroki mai suna Gizo ya bishi yana masa
roko da kirari yana neman kyauta gagaruma bisa
wannan baiwar haihuwa da Allah ya baiwa
abokinsa.

Aikuwa nan take Alhaji Dangwate yace
da marokin kaje nabaka duk kayan dake jikina da
kuɗaɗen aljihu na.. Wohoho.. Wannan abu ya isa
makura.

A lokacin ance Fam ɗari ne a aljihunsa, gashi
kuwa kusan fam ɗaya ake biyan sadakin budurwa
a lokacin. Haka kuwa bayan an gama taro Alhaji
ɗangwate ya cikawa wannan maroki alkwarinsa.

A fannin taimakon na kasa kuwa, ance akwai
wani lokaci da Alhaji Muhammadu ɗangwate ya
tura ɗansa Alhaji Garba Dangwate maiduguri
fatauci.

A wannan dalili ne sai ya haɗu da Alhaji Bukar
Bolori, wani ɗan kasuwa shahararre a maiduguri
har kuma ya nemi yasan daga ina Alhaji Garba
ɗangwate ya fito.

Daya tashi sai yake sanar masa ai sunan
mahaifinsa Alhaji Muhammadu ɗangwate.. Nan
take sai akaga jikin Alhaji Bukar Bolori yayi
sanyi.

Daga baya sai yake sanar masa da cewa ai Alhaji
Muhammadu Dangwate ne silar arzikinsa.

Domin
shine ke ɗora masa tallar kwanuka yana zagawa
ya siyar, daga bisani yace masa ya komo garinsu
zai rinka aika masa da kaya yana siyarwa.. A
Haka har ya buɗe shago nasa, ya kuma zamo
sahun attajiran Maiduguri.

Irin waɗannan labarai suna da yawa dangane da
Marigayin.

Amma dai a karshe Allah yai masa rasuwa a
shekarar 1966, ya bar 'ya'ya 15, acikinsu harda
Alhaji Aliko ɗangwate wanda yake a matsayin
Attajiri na ɗaya a faɗin Afirka.

Da fatan Allah yajikansa ya kuma kyauta namu
zuwan amin.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Sadiq Tukur Gwarzo

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: