Saturday 18 May 2024

Karanta Tatsuniyar Manomi Da Jaki

Tura Wannan Zuwa Ga

INA YARA?


GA-TA-NAN GA-TA-NANKU


Wani manomi ne yake da Jakinsa da yake hawa kullum idan zai je gona. Manomin nan na kula da jakinsa matuka. Ana ba shi abinci mai kyau da ruwa, kuma kullum ana share masa wurin kwanciyarsa. Ran nan bayan manomi ya dawo gona da jaki, ya zauna yana hutawa, Jaki kuwa yana kwance can gefe cikin inuwa, sai ga wani ɗan kwikwiyo ya zo gaban manomi yana 'yan tsalle-tsallensa na wasa yana lasar kafafun manomi. Manomi kuwa yana kallonsa yana dariya, har dai ɗan kwikwiyo ya faɗa bisa jikinsa.


Tatsuniya
Hoto: Next Avenue


Manomi ya riƙa shafa jikin ɗan kwikwiyo cikin jin daɗi, ya sa hannunsa cikin aljihu ya fito da wani abinci ya ba ɗan kwikwiyo. 


Ashe duk abin nan da ake yi Jaki da ke can gefe kwance yana kallo. Shi ma sai ya tashi yana tsalle-tsalle, kamar yadda ya ga ɗan kwikwiyo, na yi, wai shi ma ya burge mai gidansa.


Da manomi ya ga haka sai ya fara dariya, Jaki kuwa ganin ya fara shiga gun mai gida, sai ya matso ya ɗora wa mai gida ƙafafunsa, wai shi ma zai hau jikinsa kamar yadda ɗan kwikwiyo ya yi.


Ko da yaran mai gida suka ga Jaki na shirin lahanta mai gida, sai suka taso masa da kulake, suka yi ta ɗimar shi. Jaki ya gudu yana cewa: " Ashe dai inda wani ya yi rawa aka ba shi kuɗi, idan wani ya yi duka zai sha.".


KURUNGUS.


Tushe/Asali: Kundin Tsatsuba 

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user