Thursday 11 April 2019

KARSHEN TIKA-TIK: AN SAKI WASU SABABBIN VIDEOS HADIZA GABON Vs AMINA AMAL....LATEST VIDEOS

Tura Wannan Zuwa Ga
An saki sababbin Video daga Mabiya Jaruman Kannywood Hadiza Gabon Vs Amina Amal.

Mutane daban-daban daga Sassan Kasar nan dama duniya sun fadi ra'ayoyin su akan abinda Jaruma Hadiza Gabon ta yiwa Jaruma Amina Amal...


1.... Da farko dai ya kamata jama’a su sani, duk cikin bayanin da Amina Amal ta yi, babu inda ta ambaci sunan Hadiza Gabon, amma kuma ita Gabon din sai ta sha jinin jikinta ta ce da ita ta ke. To in ba rami me zai kawo maganar rami ?

Gaskiyar al’amari shi ne: dole jama’a su yarda babu karen da ba bule ba cikin wadannan jarumai biyu, in har Amina Amal ta karbi laifuffukanta na irin ‘barnar da ta ke, to wajibi ne ita ma Gabon ta yarda cewar ta na aikata abin da ta zargi kanta da shi.

Sannan kuma, a tsarin shari’a da doka, duk yadda mutum ya kai ka siffanta surarka wajen yi maka shagube da gugar zana ko danganta ka da wani laifi, babu abin da doka ta isa ta yi masa matukar bai fito ‘baro-baro ya kama sunanka ba.

A nan babu inda Amal ta siffanta ko da kamannin gabon cikin kalamanta balle inda ta kama sunan Gabon.

Amma duk da haka ta tsargu har ma ta yi mata titsiye gami da duka.

Jaruma Hadiza Gabon tare da Jaruma Amina Amal

Kuma wannan ya isa ya ba wa ‘kungiyoyin kare hakkin mata da masu kare hakkin dan adam dama su bi wa Amal hakkinta domin abin da gabon ta yi mata cin zarafi ne da keta hakkin dan adam.

Domin ko da sunanta ta kama cikin kalaman da ta yi, to ba ta da hurumin da za ta yi mata titsiye balle ta tilasta mata amsa laifi cikin duka da zagi.

Kotu ce ta ke da hurumin tuhumarta. Ba shakka wannan danyen hukunci da Gabon ta yankewa Amal, ya ci karo da doka da kuma hakkin bil’adama.

2... Duk da ba na kallon Hausa films Sosai kuma ban san da yawa daga cikin su ba.

Amma abun da naga Hadiza Gabon ta yiwa wata mai suna Amina Amal, bai kamata ba kuma ya sabawa kundin laifukan 'yancin Dan Adam ta Fuskoki 3.

Criminal case:

Wato Manyan Laifuka, Za'a iya cajin Hadiza Gabon, a karkashin sashuka da dama na kundin laifuffuka domin yin amfani da karfi, tsoratarwa, hadin baki, duka da sauran su kuma hakan zai iya bayuwa ga daure ta a gidan yari na tsawon shekaru.

Torturing:

Hadiza Gabon, na iya fuskantar biyan diya mai yawa saboda takurawa Amal da cin zarafinta da ta yi a karkashin tortuous wrong redresses.

Violation of fundamental human rights:
Haka kuma abun da aka yiwa Amal ya sabawa kariyar da dokokin kare hakkin Dan Adam suka tanada a Najeriya.

Saboda haka ya kamata hukumomi su shiga cikin wannan magana da gaggawa domin taimakawa wannan yarinya....
Kalli Videos din Kai Tsaye...3.... Kwanakin Baya Jaruma Empire Wato Hauwa Mai Maganin Mata..

Ga Daga Ido Da Ido Babu Tsoro Tayi Bidiyo A Instagram Tace Hadiza Gabon Da Laila Ali Usman Yan Lasbian Ne Kuma Suna Neman Juna Haka Kuma Tace Wallahi Hadiza Gabon Bidiyo Takema Manyan Mutane Tana Samun Kudi Dashi….

Amma Da Ike Ita Jaruma Empire Ba Sa’arsu Hadiza Gabon Bace Kunga Ai Hadiza Gabon Ko Maganar Batayi ba Domin Tasan Hauwa Jaruma Empire Tafi Karfinta Ta Ko’ina Tafi Hadiza Sanin Manya Tafi Hadiza Kudi Tafita Iya Iskanci….

Kawai Dai Hadiza Gabon Ta Samu Yar Jaririyar Yarinya A Cikin Bariki Shiyasa Tayi Mata Abinda Taga Dama A Idon Duniya…

A Dokar Kasa Amina Amal Bata zagi Hadiza Gabon ba Domin Bata Kama Suna Ba Amina Amal Kawai Harbin Iska Tayi Itakuma Hadiza Gabon Ta Ara Tayafa Ajikinta….

Sauke Video anan kasha kallon abinda ya faru da Jaruman daga Farko har karshen...

Download Video HereShafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user