Thursday 23 May 2019

Karanta Ka Ji: Wane ne Bahaushe Na Asali

Tura Wannan Zuwa

Masana na ciki da wajen ƙasar Nijeriya sun yi tsokace-tsokace masu tarin yawa a dangane da wanda ya kamata ya amsa sunan Bahaushe, a inda mafi yawa daga ciki suka bayyana cewa, "Bahaushe shi ne duk wani mutum wanda mahaifinsa da mahaifiyarsa Hausawa ne, kuma sun haife shi a ƙasar Hausa, sannan ya ɗauki harshe da al'ada da ɗabi'u na Hausawa. To wannan shi ne Bahaushe."

Kasar Hausa ta fara ne daga Arewacin Nijeriya zuwa Kudancin Jamhuriyar Nijar, wanda nan ne mazaunin Hausawa na gado.

Abdalla, (2010) Ya bayyana cewa "Duk wanda salsalarsa babu wani yaren iyaye sai Hausa, to shi ne Bahaushe. Idan a jerin iyaye da kakanni akwai wanda ba Bahaushe bane, to kai ma ba Bahaushe bane. 'Na aro wannan ma’aunin bisa cewa Hausanci ƙirar halitta ce, ba lafazi ba. Misali: A ƙasar Turawa, in a cikin iyaye da kakanninka akwai baƙar fata, to ko ka fi madara fari a matsayin bakar fata kake.

A wannan ma’aunin, babu maganar zama a wata al’umma da kuma sanin yarenta, domin ka zama ɗan wannan al’ummar. Misali: Duk iya Larabcin baƙar fatan da ya zauna a garin Maka, ba za a taɓa kiransa Balarabe ba, ba wai kawai don akwai bambancin fatar Balarabe na ainihi da baƙar fata ba, a’a, kawai ba Balarabe bane, kuma shi ma ya san haka.'

Saboda haka komai iya Hausar Babarbare da Bayerabe da Tibi da Inyamuri da Bafulatani ba zai taɓa zama Bahaushe ba, sai dai a kira su da "Hausawan Zamantakewa".

A cikin ƙamusun Hausa na Jami'ar Bayero, Kano (2006), an bayyana cewa "Bahaushe shi ne haifaffen mai magana da harshen Hausa da rayuwa irin ta Hausawa."

Tunda haka ne, yanzu a dai-dai wannan gaɓar zamu duba wasu abubuwa, mu yi nazarinsu, ta yadda za su zamo mana hoto ko madubin ƙara bayyana mana Bahaushe na ainihi. Daga cikinsu akwai:

1. HARSHE: Kamar yadda aka bayyana a cikin Ƙamusun Hausa na Jami'ar Bayero (2006), harshe na da ma'anoni daban-daban, amma ɗaya daga cikin ma'anarsa ita ce, harshe na nufin "Hanyar magana tsakanin al'umma iri ɗaya".

A saboda haka idan muka ɗauki wannan ma'ana ta harshe, zamu ga cewa dukkan wata ƙabila tana da harshe irin nata da take gudanar da harkokinta na yau da kullum da shi, kamar yadda ya zamo cewa harshen Balarabe shi ne Larabci, Bature kuma Turanci, Bayarbe kuma Yarabanci, to haka shi ma dukkan wani Bahaushe harshensa shi ne Hausa.

Umar (1981), cewa ya yi: "Hausawa su ne mutanen nan waɗanda ƙasar Hausa ce mazauninsu kuma harshen Hausa ne harshensu na asali."

Wannan bayani na ƙara tabbatar mana da harshen Hausa a matsayin harshen Bahaushe. Tuntuɓe da ɗungushe, a kan wannan batu ma (Abdalla U.A. 2010) ya ƙara bayyana cewa "Duk wanda salsalarsa babu wani yaren iyaye sai Hausa, to shi ne Bahaushe."

Harshen Hausa dai ɗaya ne, amma yana da kare-karen da kowace daula a ƙasar Hausa take da irin nata. Misali: Kananci da Sakkwatanci da Katsinanci da Zazzaganci da sauransu.

2. SIFFA: Ma'anar wannan kalma ita ce "Hanyar bayyana kamannin abu" (Ƙamusun Hausa na Jami'ar Bayero 2006). Idan an ce haka kenan zai iya kasancewa bayyana siffar dabba ne ko mutum ko wani abu makamancin haka. To amma tunda muna yin magana ne a dangane da abun da ya shafi Bahaushe, to kenan batummu zai karkata ne ga bayyana siffa ta ɗan-Adam.

Abu ne sananne a duk lokacin da aka ce Bature kai tsaye za a hasaso cewa wannan mutumin fari ne, mai kwantaccen gashi da dogon hanci da sauransu. Haka ma dai idan ka je kan Larabawa suma tasu siffar daban take. Idan mun dawo maƙotanmu na kusa wato Fulani, su ma dai zamu tarar da suna da irin tasu siffar. Misali: suna da tsawo, sirara ne masu dogon hanci da dogon wuya da zarazaran yatsu da kwantaccen gashi da sauransu. Saboda haka shi ma Bahaushe kamar sauran ƙabilu yana da irin tasa siffar, wadda take bayyana shi a matsayin Bahaushe na ainihi, kamar yadda zamu gani a halin yanzu.

Bahaushe baki ne ba fari ba, sannan kuma gajere ne ba dogo ba, kakkaura ne, faffaɗa mai cika ido. Hancin Bahaushe mai faɗi ne, kuma gajere ne bashi da tsawo kamar irin na Larabawa da Turawa ko na Fulani. Sannan kuma gashin kansa mai tauri ne da yake fitowa a nannaɗe maras yalwa, ba irin na Larabawa ko Fulani bane ba wanda ke kwantowa a gadon bayansu mai santsi da sheƙi. Su ma mata da 'ya'yan Bahaushe basu da yalwar gashi a kawunansu.

3. HALAYYA: Kamar yadda aka bayyana a cikin Ƙamusun Hausa na Jami'ar Bayero (2006), halayya na nufin "ɗabi'a, musamman ta mutum." Masana da manazarta sun bayyana halayyar Bahaushe da cewa, Bahaushe mutum ne mai halayya ta ƙwarai, abar koyi da yabawa. Sannan kuma sinadaran halayyar Bahaushe sun haɗar da:

i) ALKUNYA: Bahaushe mutum ne mai alkunya, a inda yake bayyana hakan a dukkan lokacin da wani abun kirki ya haɗa ku da shi, misalin hakan na bayyana a tsakanin mata da miji ko siriki da iyayen matarsa ko mace da sirikanta da kuma 'ya'yanta na fari. Wannan ne ma ya haifar da ɓoye suna ta yadda uwa bata iya furta sunan ɗanta na fari saboda alkunya.

ii) KAMA SANA'A: Bahaushe mutum ne mai riƙe sana'arsa da muhimmanci tun tale-tale, a inda zaka tarar da cewa kowacce sana'a har sarki ne da ita, wato shugaban duk masu yin irin wannan sana'ar, irin su noma, da kira, da farauta da rini da wanzanci da dukanci da sauransu.

iii) RIƘON ADDINI: Bahaushe mutum ne mai riko da addini, la'akari da yadda bayan ya karɓi addinin Musulunci ya rike shi hannu bibbiyu, har ya kai ga, a duk lokacin da aka ce wane Bahaushe ne, to abun da za a fara kawo wa shi ne Musulmi ne ko da kuwa ba hakan bane ba.

Sauran ire-iren sinadaran halayyar Bahaushe sun haɗar da: Adalci, da amana da dattako da gaskiya da haƙuri da hankali da hikima da juriya da jarumta da karamci da kawaici da ladabi da mutunci da rashin tsegumi da zumunta da sauransu. Ba kamar yadda wasu a yanzu suka ɗauki Bahaushe a matsayin, mutum mai munanan halaye maras ɗabi'u masu kyau ba.

Ɗabi'u da halayen Bahaushe masu kyau ne, amma haɗuwarsa da baƙin al'ummu ne ya yi sanadiyar gurɓacewar wasu daga cikin al'adu da halaye da ɗabi'unsa masu kyau da ya gado tun iyaye da kakanni, amma fa har yanzu akwai saura daga cikinsu waɗanda suka kasance a tare da shi, kamar dai yadda masu iya magana suka ce, kowa ya bar hali, ba nasa bane.

4. MUHALLI: A tsarin gidan Bahaushe, maigida shi ne shugaba a gidansa. Masana sun ƙara da cewa, duk matansa da ‘ya’yansa, da sauran yaran gida da masu yi musu hidimomi, suna ƙarƙashinsa a matsayin mabiya. Maigida ne zai ɗauki nauyin ciyar da kowane mazauni a gidan, shi ne kuma zai yi wa kowa tufafin sakawa, ya kuma ba su makwanci, haka kuma, shi ne wanda zai shirya musu irin ayyukan da kowa zai yi, ya kuma raba wa kowa nasa aikin, ya kuma tabbatar da kowa ya yi aikin
da ya ba shi. Idan ana buƙatar wani abu a gidan, shi maigidan ne za a tambaya, sai ya ba da izini kana a ɗauki abin. Haka kuma nauyin kare lafiyar mutanen gidan, da kare mutuncinsu da yi musu tarbiya duk a wuyan maigidan yake, a matsayinsa na shugaban gida.

Zaman gandu, wato gida-cikin-gida shi ne tsarin zaman Bahaushe na asali, inda yake zaune a cikin babban gida tare da magidanta fiye da goma, kowane da yankinsa a gidan, inda yake tare da rukunin iyalinsa a ƙarƙashin shugabancin Uban-gandu, wanda shi ne dattijo mafi tsufa a gidan, wanda shi ne babba a shekaru, ba wanda ya kai shi tsufa a gidan. Wannan tsoho, zai kasance a nasa rukunin tare da iyalinsa, akasari matansa da ƙananan ‘ya’yansa waɗanda ba su isa aure ba. Saura manyan magidanta, kowanne yana da nasa rukunin, inda shi ma yake zaune da nasa iyalin. Irin wannan zama, zama ne na ‘yan’uwantaka da ƙara ƙulla zumunci, da taimakon ‘yan’uwa, da haɗa kai. Saboda za ka tarar komai nasu gabaɗaya suke gudanar da shi, kawunansu a haɗe suke, suna taruwa su yi aiki gabaɗaya, misali lokacin damuna sai duk su tafi wajen gonarsu ta Gandu su haɗu su nome ta sai kuma su bi sauran gonakin ‘yan’uwa suna nomawa har su gama. Wannan irin zama, zama ne na cuɗe- ni-in-cuɗe-ka, da kuma lumana ba ƙiyayya da gaba.

Idan har yanzu mai karatu yana da kokwanto a kansa, akwai buƙatar ya ƙara fahimtar cewa, duk mutumin da ya kasance ruwa biyu, a Hausance shi ake kira “Barbarar-yanyawa.”




Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode






TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

Sunana Abba Muhammad Sagir wanda aka fi sani da Abba Danhausa. Ina son harshen Hausa sosai, kuma ina da sha'awar yin rubuce-rubuce a cikinsa. Burina a ko da yaushe kawo wa harshen Hausa ci gaba ta fannoni daban-daban na rayuwa, tare da ganin ya bunkasa, ya wuce inda yake a yau. Wannan shafin na bude shi ne domin kare martabar harshen Hausa, da ciyar da al'ummar Hausawa gaba da sauran masu ji da magana da harshen Hausa ta hanyar yin la'akari da harshe da adabi da al'adun Hausawa. 07038838301.