Saturday 11 May 2019

Karanta Kaji: Yau na kara Tabbatar da rashin Hankali da jahilcin wasu daga cikin yaran Kwankwasiyya

Tura Wannan Zuwa Ga
Lallai muddin Kwankwasiyya zata cigaba da tafiya da marasa kwakwale, to tabbas babu inda tafiyar zata karkare sai rashin nasara da kuma kara samun koma baya.


Sheikh Isa Ali Pantami



Banda rashin ilimi da toshewar kwakwale, haka kawai wasu su kirkiro karya domin rage darajar tafiyar siyasar ku, ku kuma ku kasa gane salon takun su, suna jefowa kawai kuka cabe.

Labarin da ake yadawa akan cewar Isa Ali Pantami ne ya fada, labarin karya ne domin na bibiyi tafsiran Isa Ali Pantami na azumin bana banji inda ya fadi maganar ba. Haka kuma na tuntubi makusantan shi domin sanin sahihancin zancen, suma sunce gani kawai sukayi ana watsawa a shafukan sada zumunta.


Ta inda naga toshewar kwakwalen yan Kwankwasiyya shine, yadda sukayi ca akan Isa Ali Pantami suna rugawa iyayen sa ashariya ba tare da duba makomar siyasar su awajen dumbin mabiyan Isa Ali Pantami ba.

A iya nazari da tunanina, wannan labari wasu kwararru ne suka kirkireshi domin tunzura Marasa hankali na Kwankwasiyya, da zummar neman rage daraja da mutuncin Kwankwasiyya a idon mabiya Isa Ali Pantami.

Kuma tabbas sunyi nasara domin Isa Ali Pantami da Iyaten sa sun sha zagin kare dangi agun yan Kwankwasiyya, su kuma mabiya Isa Ali Pantami wadanda suke ganin Kwankwasiyya da mutunci sun dawo daga rakiyar ta.



Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode






Source:  HAJI SHEHU


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user