Sunday 2 June 2019

KARANTA TAKAITACCEN TARIHIN ASALIN FULANI: ABUBUWAN DA BAKU SANI BA GAME DA ASALIN FULANI

Tura Wannan Zuwa
Mal Ahmad Usman Bello, shugaban kungiyar Fulani ta kasa mai suna FULDAN, bafullatani me Batoranke, kuma masani akan tarihin jinsin sa, a wata zantawa da mukayi dashi ya faɗa mana wasu ƙarin mahangai game da tarihin Fulani.Tarihin Asalin FulaniMarubuciSadiq Tukur GwarzoASALIN KALMAR FULANIDa fari dai, masanin ya faɗa cewar tabbataccen tarihi shine wanda yazo a Alkur'ani da Hadisai, amma duk wani abu wanda ba shiba kan iya zamowa gurɓatacce, don haka bai ɗoru akan cewa wajibin duk abinda ya faɗa shine na gaskiya ba.


A cewar sa asalin sunan Fulani shine Tuta (Futa Toro), kuma suna cikin tsoffin kabilun duniya ne. Shi sunan Futa din sun samo shine daga kakansu/uban su da ake kira Futa, kuma shi jika ne ga Annabi Nuhu. Ta wajensa aka samar da Samudawa da Adawa, don haka faɗin Ta Ala a Alkurani (IRAMA ZA TUL IMAAD) da kabilar su yake, domin an samu cewa an taɓa kiran su da suna Iramawa.


Daga bisanin saboda yawaitar su ga yake-yake, sai aka rinka kiransu da suna Fatah, ma'ana Jarumai. Sannu a hankali kuma aka koma ambaton su da suna Futa.


Yanayin zaman su a wurare kuwa shine silar sauyawar sunayen su, ta yadda ake kiran wasu Futa Toro, ma'ana Futawa mazaunan Toro, da Futa Masina, Futa Jallo, Futa Falgo da sauran su


A cewar masanin, shi wannan sunan na FULANI, ya samo asali ne a yammacin afirka, sanda suka haɗu da kabilar MANDINKA wajen zama, waɗanda suma kusan fulani ne a halaye da ɗabiu.


Mallam Ahmad ya tafi akan cewa Fulani kabilar farko ce da suka soma zaman Afirka, kuma sune suka zo da addini yammacin Afirka, amma fa addinin Yahudanci. Shikuwa kowa ya sani addini ne na jinsi, ba na kowa da kowa ba.


Don haka idan fulanin sun tara ƴaƴan su, su kan sanar musu da cewa 'Ana Hulɓe (Fulɓe) Allah'. Ma'ana mu masu tsoron Allah ne, kada kuyi abinda Mandinkawa abokan zaman mu suke aikatawa. Daga nan sai mandinkawa masu zuwa ganin su suka rinka kiransu da suna Fulah, kafin daga bisani sunan ya rinka sauyawa zuwa Fullata, da Fulɓe.


ASALIN BAFILLATANI MAHANGA TA ƊAYA


Mallam Ahmad ya sanar mana da cewa Bafillatani ya samu ne daga jikin Annabi Nuhu A S.


Asalin zuriyar sa kuma a yankin Ɗurun Sinin take da zama. Anan ne har Annabi Musa A.S ya riske su a zamanin sa lokacin da aka saukar masa da Attaurah. A lokacin suna masu bautar shanu, don haka sai ya kira iya kabilar sa Bani Israila zuwa bautar Allah makaɗaici.


Shiyasa sai Bani Isra'ila suka yi kwaɗayin a sanya musu abin bauta kamar yadda futawa suke yi, har kuma Musa Samiri ya shagaltar dasu tare da sanya musu ɗan mariki a matsayin abin bautar Annabi Musa A .S.


Sai daga baya Annabin Allah Musa ya gane lamarin, sannan ya kira shugaban su mai suna Tori ya karbi addini, shine har akayi bikin karɓar sa ranar asabar a jikin dutsen Ɗuri Sina. Fulani na kiran bikin 'Larki'. Har kuma sukan ce "RaduTori Sinin", watau ga Inda Tori ya musulunta wajen nuni da Ɗuri Sinin.


A wannan zamanin, sai kabilar Futah ta kasu. Wasu suka karbi addinin Annabi Musa bisa biyayya da shugaban su Tori, wasu kuma suka bijere, inda sukayi Hijira zuwa Afirka ta Kudu, daga jikin su kabilun Chusi da ake kira Totsi yanzu suka fita, da sauran kabilun da suka mamaye yankunan.


ASALIN BAFILLATANI MAHANGA TA BIYU


Akace asalin Fulani tare da Yahudawa suke da zama. Don haka kusancin su ke sanyawa ake kiransu da sunan Yahudawa. Kuma su mayaƙa ne mara sa tsoro waɗanda basa rabo da makami, sannan suna matukar ɗaukaka ranar asabar sama da sauran ranaku saboda tarayyar su da yahudawa. Sannu a hankali suka famtsama yankin Afirka ta Yamma.


ASALIN FULANI MAHANGA TA UKU


Wannan mahangar kuma ta nuna cewa Fulani tsatso ne daga zuriyar Annabi Ayyuba A.S..

Akace a lokacin da ya zama dattijo yana wa'azi a gefen tekun Indiya, sai aka bashi wata mace aure wadda bata son sa. Don hakan idan dare yayi sai ta guje masa zuwa bayan ɗaki, acan kuma sai sheɗan ya rinka zuwar mata yana tarawa da ita. A haka har ta samu rabon yaro namiji wanda baya magana da kowa.


Akayi magana akan yadda ta samu wannan yaro dube da rashin tarayyar ta da maigidanta, amma Annabi Nuhu yace a kyale ta a matsayin matar sa, daga bisani hakan ya cigaba da faruwa har ta sake haifar yarinya mace.


Don haka waɗannan mace da namijin da suka girma sune suka fara amfani da yaren su sabo na Fulatanci.


RUBUTUKA MASU ALAKA:


KARANTA TAKAITACCEN TARIHIN ASALIN FULANI SULLUBAWA:  ABUBUWAN DA BAKU SANI BA GAME DA ASALIN FULANI SULLUBAWATAKAITACCEN TARIHIN ATTAJIRIN DA YAFI KOWA KUDI A DUNIYA

TAKAITACCEN TARIHIN SHEIKH JA'AFAR MAHMOUD ADAM

TAKAITACCEN TARIHIN YAKIN BIAFRA


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user