Friday 19 July 2019

KARANTA SHARUDDAN YIN SALLAH

Tura Wannan Zuwa Ga
Sharuddan sallah sune:-

1. Musulunci. (ba ta inganta ga wanda ba Musulmi ba).

2. Hankali (ba ta inganta ga mara hankali).

3. Tsarkin dauda: Shine tsarkake jiki da tufa da bugire na mai sallah tun daga farawa har kammalawa.

Yayin Sujjada a cikin Sallah

4. Tsarkin Hadasi: Shine duk abin da ke warware alwala, shima tun daga fara sallah har zuwa kammalawa. Ana bukatar wadannan tsarki a cikin kowace irin sallah ma’abociyar raku’i da kuma sujjada kai har ma wanin nan nata.

5. Shigar lokacin sallah.

6. Niyya.

7. Sitirce al’aurar namiji tana kamawa ne daga cibiya har zuwa guiwa. Ita kuwa mace baki dayan jikinta al’aurane ga ajnabinta sai dai fuskarta da tafukan hannuwanta.

8. Fuskartar Alkibla; Sai dai in a halin rincabewar yaki ko nafila a tafiyar da ya halatta ayi kasaru kuma mutum ya zamo mahayi ne kan abin hawa.

KARANTA YADDA AKE YIN SALLAH

Wanda ya yi sallah yana kallon watan alkibla ba yana mai mantawa ko rashin sani har sai da ya yi sallama, to ya saketa har abada, sai dai malamai sun yi sabani a cikin wannan hukunci, haka hukuncin ya ke idan ya zamo bai yi sani da alkiblar ba ko ya ganganta yin sallar ba a alkiblar ba.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user