Monday 1 July 2019

KARANTA KA JI: TUNDA NAKE BANKO TABAJIN LABARI MAI BAN TAUSAYI IRIN WANNAN BA

Tura Wannan Zuwa Ga
Wata rana wani mutum ya sayi sabuwar mota daga sayanta yazo kofar gida yai packing, bayan ya shiga gida ya fito sai ya
tarar da dansa yana rubutu a jikin motar tasa nan take uban yaron ya hau yaron da bugu kamar zai kashe shi akan yayi mai rubutu ajikin mota.


Labari mai ban Tausayi


Ya kama yaron ya daure masa hannuwa ta baya yayimai dauri goro, ya dauke shi ya saka a wani daki ya kulle ya tafi da dan mabudin.

Uwar yaron tanata kuka tarasa yadda zatayi ta bude dakin ta kwanceshi, haka tanaji dan nata yana kuka tun yana kuka har yagaji ya daina.

Bayan wani lokaci mai tsawo uban Zuciyarsa ta sauko sai yadawo domin ya kwance yaron koda ya bude dakin ya sami dan nasa a sume ko motsi baya iyayi nan take ya dauke shi zuwa asibiti.

Bayan likitoci sun kammala
bincike sai suka shaidawa
uban yaron cewa sai an yanke hannuwan yaron sakamakon dadewa da yayi a daure.

Haka uban yasa hannu a takarda aka yanke hannuwan dan nashi.

Bayan wani lokaci yaron ya farfado daga aikin da akayi masa sai uban nasa ya shigo domin yaga dan nasa yana shigowa
suka hada ido da yaron, sai yaron ya fashe da kuka yace "BABA DAN ALLAH KAYI
HAKURI KA DAWOMIN DA
HANNUNA BAZAN KARA MAKA
RUBUTU A JIKIN MOTAR KABA".


Nan take da uban da likitoci da duk wanda ke wajen kowa ya
fashe da kuka.


Labari mai ban Tausayi


Bayan mutumin yafita waje sai
ya tsaya ya kalli rubutun da dan nasa yayi da kyau sai yaga yaron ya rubuta "I LOVE U DADDY".


Nan take uban ya kara fashewa da kuka.


Ya matsa kusa da motar ya taba rubun sai yaga yana gogewa ashe bai lalata paint din motar ba Allahu'akbar saurin fushi ke nan.


LABARAI MASU ALAKA:


KARANTA CIKAKKEN LABARIN SOYAYYAR LAILA MAJNUN 


LABARIN WASU SAMARI MAI HAKURI YA KAN DAFA DUTSE


LABARIN SOYAYYAR KHALIFA DA SAUDAT
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user