Thursday 5 September 2019

Ministan Sadarwa Ya Bayar da Umarnin yin Bincike akan Dalilin da Yasa ake Kwashewa 'Yan Nigeria Data da Kudin Kira ba Bisa Ka'ida Ba

Tura Wannan Zuwa Ga
Maigirma Ministan Sadarwa na Kasarmu Nigeria Ash-sheikh Dr Isa Ali Ibrahim Pantami, ya rabawa shugabannin hukumomin da ke karkashin ma’aikatar Sadarawa aikin da zasu yi.

Yakamata a Jinjinawa Dr. Isa Ali Pantami


Marubuci: Datti Assalafy

Ministan ya bayyana cewa za'a bawa kowace ma’aikata aikin da ake so ta yi zuwa wani lokaci, inda za'a rika bibiyan kokarin da kowane shugaba ya ke yi domin sauke nauyin dake kan sa.

1- Hukumar NCC: Ma’aikatar sadarwa ta bawa NCC lokaci ta kawo karshen matsalar rashin yiwa layukan waya cikakken rajista wanda yin hakan zai inganta tsaro, an kuma nemi NCC ta duba yadda ake zaftarewa jama’a kudin hawa yanar gizo tare da rage kudin sayan data ba bisa ka'ida ba, sai kuma kudin da ake cirewa a kiran waya.

2- Kamfanin Galaxy Backbone GBB: Daga cikin aikin da aka bawa wannan kamfanin shine su gyara karfin layinsu da sauran ayyukan da su ke yiwa jama’a.

3- Hukumar NITDA Sheikh Isa Pantami ya nemi magajin sa a NITDA Malam Kashifu Inuwa ya dage wajen ganin an samu karuwar masu amfani da na’urorin fasaha da manhajojin gida a ma’aikatu, Ana kuma so ma’aikatu su rika amfani da na’urorin zamani wajen aikinsu.

4- Hukumar NIGSAT: Hukumar NIGSAT mai kula da lamuran tauraron 'dan adam (Satellite) na Nigeria, Maigirma Minista ya umarci babban darakta a ma'aikatar da kara kaimi sun tabbata tauraron 'dan adam na haska kowani sassa na Kasar Nigeria, sannan su kawo cigaba a aikinsu.

5- Hukumar NIPOST:Sabon Ministan sadarwa ya nemi NIPOST ta kara kokari wajen aika sakonni da wasiku a fadin kasar, ya kuma bada umarni ga hukumar ta kara yawan guraren da ta ke shiga a cikin Kasar Nigeria lunguna da sako.

Yaa Allah ga bawanKa nan Ministan sadarwa na Kasarmu Nigeria yana da burin kawo canji mai ma'ana, Ubangiji Allah Ka taimakeshi, Ka hadashi da mashawarta na gari, Ka cika masa burinsa na alheri Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user