Tuesday 12 November 2019

Na so ace Mahaifiya ta tana raye don taga yaron da na haifa - Maryam Bukar 'Yar Jaruma Hauwa Maina

Tura Wannan Zuwa Ga
Maryam Bukar Daya da ga cikin yara matan da ake alfahari da su a Arewacin Najeriya ta fannin kokarin yada da’awar addinin musulunci cikin harshen turanci ta hanyar zantukan azanci da karin magana da Turawa ke kira da ‘poetry’.


Na so ace mahaifiya ta na raye don taga yaron da na haifa

Maryam wadda a ka fi sani da Alhanislam ‘ya ce ga fitatciyar Jarumar Finafinan Hausa, Marigayiya Hajiya Hauwa Maina.

A hirar da muka yi da Maryam ta bayyana mana cewa Allah ya fara haskaka ta ne tun mahaifiyar ta na raye, inda take cewa tabbas ta yi babban rashi na rasuwar mahaifiyar ta amma alhamdulillahi tunda ta rabu da ita lafiya sun rabu tana mai mata addu'a da kuma sa mata albarka.

“Mahafiya ta tayi matukar kokari wajen ganin na samu ilimi mai kyau. wanda ko ita bata samu ba musamman na bangaren addini.” In ji Ahlanislam

Hauwa Maina yar fim ce wadda ta yi shura wajen iya taka kowanne irin matsayi wanda bai sabawa tarbiya ba. Ta kan so fitowa a bangaren addini ko da'awa. Kuma Maryam ta shaida mana cewar mahaifiyar ta ta, ta zuba hannun jari a hanyoyin fadada addinin musulunci da yawa.

”Mahaifiyata ta bada gudunmawa wajen karfafa mun gwuiwa ta ga na fara harkokin da'adawa, har ta bude tsangayar wayar wa jama'a kai akan harkokin addini mai suna ‘Deen Atat Foundation’ ita ta ke daukar nauyin komai wanda ba kowa ya sa ni ba." Inji Maryam Bukar

Maryam ta kasance mai sha’awar ta gaji mahaifiyar ta a kan harkokin ta wanda ya hada har da fitowa a cikin finafinan Hausa.

A baya bayan nan ne a ka ganta ta fito a wani fim Mai dogon zango mai suna MUQABALA wanda Usman Uzee ya shirya.

Alhanislam ta yi aure da kuruciyarta cikin kwanciyar hankali. Kuma aurenta bai hana ta sabgogin da ta saba ba har ma da samun goyon baya daga wajen mijinta. Hakan ya sa ta yi kira ga yan uwanta mata da su yi aure indai sun samu miji na gari wanda hankalin su ya kwanta da shi. Ta kara da cewa suyi addu'a har Allah ya basu irin wanda suke so, kar kasuwancin da su ke ko wata sana’ar ta hana su aure.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Ana Zargin Mawaki Nura M. Inuwa Dacin Hakkin Al'umma...Latest Video

Mafi Yawancin Mazajen da Suke Son 'Yam Matan Kannywood Mayaudara Ne - Jaruma Maimuna Muhammad

Kalli Hotunan Matar Jarumi Adam A. Zango Wadanda suka Haifar da Cece-Kuce a Shafukan Sada Zumunta

“Na so ace mahaifiya ta na raye don taga yaron da na haifa, wato jikan ta. Gaskiya ba ni da wani mafarki da ya wuce haka a rayuwata amma kuma Allah Bai so ba.”

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeSource: NORTHFLIX
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user