Wednesday 26 February 2020

Karanta Bambancin Soyayyar Facebook da Soyayyar Zahiri

Tura Wannan Zuwa Ga
Bambancin soyayyar facebook da soyayyar zahiri, shine silar haɗuwa.

Soyayyar Facebook da Soyayyar Zahiri

Marubuci: Fakihu M. Sani Jinkir

Soyayyar Zahiri sun haɗu ne a zahiri kowa ya ga kowa, Soyayyar Facebook kuma soyayyar badili ce, sun haɗu ne ta hanyar rubutattun saƙonni wanda suke tura ma junan su ta hanyar charting.

Soyayyar Facebook tana da ƙalubale masu yawa fiye da soyayyar zahiri, duk auren da silar ƙulluwan sa Facebook ne, zai yi wahala kaji ya mutu, saboda auren soyayyar facebook mutane masu gaskiya da amana ne suke yinsa, shi yasa mafi yawanci zaka ga idan auren bazai yiwu ba tun kafin suga juna a zahiri soyayyar take watsewa saboda ɗaya yana cin amanar ɗaya, ko kuma suna cin amanar junan su, ta hanyar soyayya da wasu a zahiri bayan wanda suke soyayyar facebook da shi/ita.

Soyayyar zahiri tafi soyayyar facebook tasiri.

Auren soyayyar facebook yafi auren haɗuwar zahiri nagarta.

Idan kaga wasu sun haɗu a facebook har sunyi aure toh ka tabbata soyayya ce ta tsakani da Allah, Dan Allah suke son junan su.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user