Wednesday 26 February 2020

Ku Kiyayi Kan Ku da Ciwon Hassada

Tura Wannan Zuwa Ga
Yana daga cikin mummunan ciwon da ya addabi al'ummah a wannan lokacin kuma mutane sun ƙi su farga sai kisa yake  ba dare ba rana, ciwon hassada.

Hassada Mugun Ciwo!!!



Me hassada tamkar yana fito na fito ne da mahaliccin sa.

Me hassada tamkar yana ƙalubalantar Allah ne a kan bai iya  hukunci ba.

Me hassada burin sa ni'imar da Allah ya yiwa wanin sa ta kife  kar ta kai izuwa gare shi.

Me hassada yana rayuwa cikin ɓacin rai baƙin ciki damuwa da ƙuncin zuciya.

Me hassada yana asarar ladan  sallar sa, A azumin sa da duk ayyukan sa na alkhairi.  

Me hassada bai isa ya cutar da wanda yake wa hassada ba don  Allah ne  yayi hukuncin.

Da me hassada zai gane shima sai ya nema daga falalar Allah idan Allah yaga dama  Sai shima ya samma sa.

YA ALLAH YA KARE MU DAGA YIN HASADA A KAN NI'IMOMIN DA YAYI WA BAYIN SA, SANNAN YA KARE MU DAGA DUKKAN SHARRIN MA SUYI MANA HASSADA AMIN.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user