Tuesday 3 March 2020

Na Kammala Karatu Amma Babu Aikin Yi Me Zanyi?

Tura Wannan Zuwa Ga
Ba abin kunya ba ne budurawarka ta ganka kana tura baro kana neman abin da za ka sanya a bakinka da rufawa kanka asiri.

Yi Amfani da Damar Ka..

Marubuci: Abbati Mai Shago Flg

Kada ka ce za ka raina ƙaramar sana'a don kana ganin kana da babbar takardar bayan ka nemi aiki ka rasa, ka yi haƙuri ɗan uwana ka nemi abin da za ka riƙa samun kuɗin shiga ko da kuwa zuwa daji kana yo itace kana sayarwa ne wata rana sai labari; kana tsaka da aikinka za a ce ana buƙatar takarda irin ta taka, kada baƙin cikin ƙin samun abin da kake so ya jefa ka cikin mummunan hali, ba fa za ka koma ga mahaliccinka ba har sai ka cinye arzikinka gaba ɗayansa.

Allah ka bawa matasanmu abin yi, ka cire musu raina abin da ake samu a cikin ƙananan sana'o'i, ka faɗaɗa musu samun su, ka wadata su daga falalarka Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user