Monday 9 March 2020

KARANTA MATSALAR MASOYA A YAU

Tura Wannan Zuwa Ga
Matsalar masoya ayau kusan itace amfani da dama ko iko! Wato duk ɓarawon (masoyin) da ya lura cewa ɗaya ɓarawon yafi sonsa, kuma yana masa tsantsar soyayya, sai ya riƙi wannan a matsayin hanya ko makami na wahalar dashi.

Matsalar Rayuwar Masoya a Yau..

Marubuci: Adam Abu-Umayrah

Karshe har ya dinga zubar masa da ƙima a idon Al-umma, ganin kawai ya mallaki zuciyarsa a hannunsa, komai darajar wancan ɓangaren ko ƙimarsa kuwa a idon Al-umma, wannan hali ya riga ya zama ruwan dare tsakanin maza da mata, wasu kuma sai su maida wannan dama wata sitiyari da zasu dinga tanƙwara wancan ɓarawon ƙarfi da yaji!

Wannan mummunan hali sai ya tunamin da baitin Umru'ul Qais inda yake kokawa gameda abar begensa ba.

Yake cewa:

ﺃﻏﺮﻙ ﻣﻨﻲ ﺃﻥ ﺣﺒﻚ ﻗﺎﺗﻠﻲ # ﻭﺃﻧﻚ ﻣﻬﻤﻰ ﺗﺄﻣﺮﻯ
 ﺍﻟﻘﻠﺐ ﻳﻔﻌﻞ !

(KE YANZU GANIN CEWA SOYAYYARKI ZATA KASHENI YA RUƊEKI, DA KUMA GANIN CEWA DUK ABINDA KIKA UMARTA ZAN AIKATA)

Soyayya gaba ɗaya dakon wahala ce, sai wanda Allah yayiwa gyadɗar dogo!

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: