Tuesday 10 March 2020

Ku Kiyaye Halayyar Mutane

Tura Wannan Zuwa Ga
Hadith ya tabbata daga Mu’az Ɗan Jabal cewa: Manzon ALLAH (ﷺ) Yace: “ku nemi taimako bisa biyan buƙatunku da ɓoyewa, lallai duk ma’abocin ni’ima yana da mahassada.” [Dabarani ya ruwaito shi, Albany ya inganta shi cikin Assahiha 3/436. Hadith na 1453].


Kaji Tsoron Mutam ka Kuma Ji Tsoron Allah

MarubuciyaFaridah Bintu Salis

Idan za kayi tafiya, kayi tafiyarka, ba sai ka shelantawa mutane ba.

Kayi rayuwarka ta soyayya cikin gaskiya da amana ba sai ka yi ta yamiɗiɗi da maganar a cikin mutane ba.

Kayi rayuwarka cikin jin daɗi, walwala da natsuwar zuciya, ba sai ka faɗa wa kowa ba.

Domin ka sani mutane da dama sun fi ƙoƙari wajen ganin lalacewar rayuwarka ba ci-gaban ka ba, musamman a wannan zamanin muna cikin lokacin da ya kamata mutane su ringa kiyaye sirrukan rayuwar su.

ALLAH Yayi mana katangar ƙarfe da dukkan abunda zai cutar damu ya Kuma datar damu da dukkan abunda yake alkhairi ga rayuwar mu Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: