Wednesday 11 March 2020

Amfanin Kasancewa Da Abokai Nagari A Ranar Hisabi

Tura Wannan Zuwa Ga
Manzon Allah (صلى الله عليه وآله وسلم) Yace:

“Lallai haƙiƙa idan 'yan Aljannah suka shiga Aljannah, sai kuma ya zamto basu samu abokanansu (a cikin Aljannar) ba, waɗanda suka kasance suna tare da su akan (ayyukan) alkhairi a (gidan) Duniya”.

Kayi Abota da Mutanan Kirki

Marubuci: Auwal Aliyu Sara

”To, Lallai haƙiƙa za su nemi (a ba su) cetonsu”.

Sai suce:

“Ya Ubangiji! Haƙiƙa muna da 'yan uwa, waɗanda suka kasance suna yin Sallah a tare da mu, kuma suna yin Azumi a tare da mu, amma kuma ba mu gansu (a cikin Aljannah) ba”.

Sai Allah Mai buwaya da ɗaukaka Yace (da Mala'ikunSa):

“Ku tafi zuwa ga (gidan) Wuta, ku fitar da duk wanda ya kasance akwai misalin ƙwayar zarra na Imani a cikin zuciyarsa”.

[Al-Silsilah As-Saheehah].

Ya 'yan uwa na masu girma!

Ina roƙon wata alfarma a wajenku: Don girma idan baku ganni a cikin (........).

Ku ce: Ya Ubangiji!

"Akwai abokinmu mai suna; Auwal Aliyu Sara , wanda mu kasance tare da shi a gidan Duniya a cikin ayyukan alkhairi, amma kuma ba mu gan shi a cikin  (.........) ba, Ya Ubangiji! Ka ba mu cetonsa".

Don girman Allah ku tuna da ni! Don girman Allah ku tuna da ni!! Don girman Allah ku tuna da ni!!!

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: