Tuesday 14 April 2020

Gaskiyar Lamari Dangane Da Cutar Sarkewar Numfashi A Nigeria

Tura Wannan Zuwa Ga
Zai yi wuya a ce a duk jihohin Najeriya 36 har zuwa yau da zaman gida na sati 2 ke kammala a ce masu cutar na jihohi 19 ne kawai saura jahohi sun sha.

Gaskiyar Lamari Game da Cutar Covid-19...

Marubuciya:- Rahma Abdulmajid


Sam ba ina wannan magana ba ne don ina masu fata ba sai don duba wasu hujjoji kamar haka:

1. Lagos, Abuja, Kaduna kusan su ne yankunan da suke da cutar tun a sati 2 baya, kuma su ne kusan mahaɗar ƙasar ta hanyoyin zirga-zirga, fatauci, aiyukan gwamnati waɗanda talaka da me kuɗi a duk faɗin Najeriya ba ya iya wadatuwa da su. Za a iya killace cutar idan ta ɓulla a jihar Bayelsa ko Maiduguri, Ko Sokoto, ko makamantan wannan jahohi da ke gefe ɗaya a Map ɗin ƙasar haka ma a harƙallar tattalin arziki. Amma ba a Kaduna ko Lagos ko Abuja ba.

2. Cutar ba kamar Ebola ba ce wadda me ɗauke da ita baya fara yaɗa ta har sai ya ji alamominta a jikinsa. Cuta ce da wataƙil tana jikinka ma tun baka ji sunanta ba ka ke yaɗawa. Kada ku yi mamaki, direbobi da dama da ba sa jin labarai sun ɗauko mutane daga Airport masu cutar ba tare da sun sani ba, kuma suka yaɗa ta. Don haka zargin mutane da cewa suna yaɗa cutar da gangan abin a yi taka tsantsan ne domin wani bai sani ba. Hasali ma  a matakin farko hukuma ce ya kamata a ce ta ɗauki nauyin killace mutane da rage zirga zirga.

3. Matsalar gwaji na da kaso mafi tsoka wajen ɓoye cutar a jihohi. Zan bayar da misalai biyu:

A. Kada ku ji kullun ana zaƙulo masu ɗauke da cutar a kullum a jahar Lagos ku zaci saboda a can cutar ta fara ɓulla ne. Sam! Saboda Lagos ɗin na da wajajen gwajin cutar ne guda tara da suke gwaji a duk ranar duniya kusan mutum hamsin a yayinda a Katsina har yau ba a bayar da samfurin mutum hamsin a ilahirin sati 3 ba! Sannan har ila yau mutanen jahar sun waye da matakan miƙa kai da sun ji alama, hakan bai ishi jahar ba don yanzu haka ta fara ƙaddamar da shirin shiga gida-gida don zaƙulo masu cutar.

Amma ilahirin Arewa idan aka cire Abuja to sai shekaran jiya waccan ne aka sami wajen awo ɗaya tal a duk faɗin jihar Kano.

B. Zuwa yanzu ƙasar Najeriya me kusan mutum Milyan 200 ta iya auna mutane dubu 5 ne kacal tun bayan ɓullar cutar.

Wannan adadi yayi kaɗan har a matakin jaha idan za mu yi la'akari da ƙasar Africa ta Kudu mai mutum ƙasa da  Milyan 60 amma tuni ta yi gwaji kan mutum Dubu 73 kuma tana ƙorafin adadin yayi kaɗan.

Waɗannan misalan na nuna idan har a mutum dubu biyar za a sami masu ɗauke da cutar har  ɗari uku da sha takwas kenan da an zage damtse an auna mutum dubu ɗari wataƙil muna da aƙalla masu ɗauke da cutar dubu shida da yan kai!

Waɗannan dalilan da ma wasu babu abinda suke tabbatar mana illa mu kare kanmu domin cutar na cunkushe a ko ina, awo da bin diddigin tona asirinta  ne ya yi ƙaranci abinda ya janyo ƙasashen waje ke ta sintirin ɗebe mutanensu daga Najeriya, ganin cewa ko masu ɗauke da cutar ba ma iya tantancewa balle a yi batun jinya, sai uban sayen Gadaje da fafatawa da talakawa kan tallafin abinci.

Allah Ya kare Mu Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user