Wednesday 15 April 2020

Shin Ko Kana Tunawa Da Wannan A Duk Lokacin Da Zaka Shaki Numfashi?

Tura Wannan Zuwa
Ai wato jama 'a idan kogi ya ƙafe asirin kifi tonuwa yake, amma fa kafin hakan ta faru ko wacce daƙiƙa da ɗan adam zai shaƙi numfashi damar tuba ce gare shi.

Dama Ce A Gare Ka...

Marubuci:- Muhammad Bello Danja

Karƙashin ayoyinnan na suratu zumar tun daga inda ubangiji yake cewa manzonsa (S.A.W);

"Kace ya ku bayina da suke tafka mummunar ɓarna a rayuwarsu, kada ku cire rai daga rahamar Allah, lallai Allah yana gafarta zunubi bakiɗaya, Allah mai gafarane kuma mai rahama" har zuwa ƙarshen ayoyin.

Ya ƴan uwa a duk lokacin da muka tsinci kanmu a halin wata jarrabawa kwatankwacin ko irin wadda wannan 'yar dirama ta faɗa (MARYAM BOOTH), maimakon muyi ƙoƙarin kare kanmu ko gamsar da ƴan uwanmu mutane waɗanda suma ba ma'asumai bane, kamata yayi muyi ƙoƙarin neman gafarar Allah da yardarsa domin itace kaɗai hanyar da zamu tsira anan duniya da kuma gobe ƙiyama.

Idan mun haɗu da Allah, muna roƙon Allah ya gafarta mana zunubanmu ya lulluɓe mu da rufin asirinsa da rahamarsa Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user