Friday 10 April 2020

Karanta Nasihohin Da Zasu Amfane Ka A Duniya da Lahira

Tura Wannan Zuwa
Waɗannan nasihohi ne guda goma, domin tunatarwa da faɗakarwa a gare mu baki ɗaya.

Kayi Ma Kanka Tanadi...

Marubuciya: Faridah Bintu Salis

1. Ka kiyaye salloli biyar akan lokaci kuma ka kula da tsayuwar dare da sallar walaha koda raka'a biyu ce.


2. Ka dage wajen karanta abunda ya sauwaƙa gareka daga AL-KUR'ANI a kowacce rana kuma ka yawaita salati ga Annabi (ﷺ).

3. Ka bada zakkar da aka wajabta maka kuma kayi ƙoƙarin yin sadaƙa a kowace rana koda da ɓarin dabino ne, idan kuma baka samu iko ba to kayita da kalma mai daɗi, ka azumci ramadan da kuma kwanaki uku daga kowanne wata ko kuma azumtar Litinin da Alhamis.

4. Idan kana son ka kasance cikin waɗanda ALLAH yake sonsu, to kaso Annabinka (ﷺ) da ahlin gidansa kuma ka kyautatawa mahaifanka.

5. Idan kana so ka zama daga cikin waɗanda idan ɗayansu yace: "Ya Ubangijina, Ya Ubangijina". sai ALLAH (S.W.T) Yace: "Na amsa kiranka bawana roƙi abunda kake so a baka". idan kana son haka? To ka kyautata abincinka ya zama na halal, kayi adalci tsakaninka da mutane kuma kayi kyakkyawar mu'amala da kyawawan halaye.

6. Idan kana so ka zama daga cikin waɗanda ake amsa addu'arsu da kuma takardunsu ta yadda zasu ringa walwalin haske ranar alƙiyama, to ka tsarkake zuciyarka, ka yawaita fadin:

ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ

Ka nemi gafara daga zunubanka ka nema ga muminai mata da muminai maza kada ka zama daga masu gafala ga barin ambaton ALLAH.

7. Idan kana so ka shiga sahun masu yabon ALLAH masu gode masa kuma ababen kusanta gare shi. To ka sani idan bawa yace: "Dukkan Yabo ya tabbata ga ALLAH". sai ALLAH yace: "Bawana ya yabe ni ya gode mini".

Saboda haka mu yawaita faɗin:

ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﻭ ﺳﻼﻡ ﻋﻠﻰ ﻋﺒﺎﺩﻩ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺍﺻﻄﻔﻰ .

MA'ANA: "Dukkan godiya ta tabbata ga ALLAH, Aminci ya tabbata ga bayinsa da ya zaɓa".

8. Idan kana son ka shiga sahun masu godiya kuma ALLAH Ya inganta zuriyarka, to ka dage da karanta waɗannan addu'o'in godiya masu zuwa:

 ﺭﺏ ﺃﻭﺯﻋﻨﻲ ﺃﻥ ﺃﺷﻜﺮ ﻧﻌﻤﺘﻚ ﺍﻟﺘﻲ ﺃﻧﻌﻤﺖ ﻋﻠﻲ ﻭﻋﻠﻰ ﻭﻟﺪﻱ ﻭﺃﻥ ﺃﻋﻤﻞ ﺻﺎﻟﺤﺎ ﺗﺮﺿﺎﻩ ﻭﺃﺩﺧﻠﻨﻲ ﺑﺮﺣﻤﺘﻚ ﻓﻲ ﻋﺒﺎﺩﻙ ﺍﻟﺼﺎﻟﺤﻴﻦ .

MA'ANA: "Ya Ubangijina ka kimtsa mini (ikon) na gode ga ni'imarka da kayi mini kuma kayi ga iyayena da kuma ikon nayi aiki nagari wanda zaka yarda dashi kuma ka shigar dani da rahamar ka cikin bayinka nagari".

 ﺭﺏ ﺃﻭﺯﻋﻨﻲ ﺃﻥ ﺃﺷﻜﺮ ﻧﻌﻤﺘﻚ ﺍﻟﺘﻲ ﺃﻧﻌﻤﺖ ﻋﻠﻲ ﻭﻋﻠﻰ ﻭﺍﻟﺪﻱ ﻭﺃﻥ ﺃﻋﻤﻞ ﺻﺎﻟﺤﺎ ﺗﺮﺿﺎﻩ ﻭﺃﺻﻠﺢ ﻟﻲ ﻓﻲ ﺫﺭﻳﺘﻲ ﺇﻧﻲ ﺗﺒﺖ ﺇﻟﻴﻚ ﻭﺇﻧﻲ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ .

MA'ANA: "Ya Ubangijina ka kimtsa mini (ikon) nagode maka ga ni'imar da kayi mini kuma kayi ga iyayena da ikon nayi aiki nagari wanda zaka yarda dashi ka inganta mini zuriyata lallai ni na tuba zuwa gareka kuma lallai ni ina daga cikin musulmai (masu miƙa wuya gareka)".

9. Idan kana son ALLAH ya shiryar da kai ga abunda zai hada maka kyautatuwar duniyarka da lahirarka, to ka dage gwargodon ikonka wajen aiwatar da umurnin ALLAH (S.W.T) kamar yadda yace: ,"Yaku waɗanda kuka yi imani kuyi ruku'u kuyi sujjada ku aikata alkhairi domin ku tsira". [Suratul Hajji aya ta 77]

10. Idan kana so ALLAH ya shiryar da kai ga tushen  kowanne alkhairi, to kace: "Nayi imani da ALLAH, Sannan ka daidaita".

ALHAMDULILLAH!!!

Ya ALLAH Muna roƙonka da kyawawan sunayenka ka bamu ikon aiwatar da ayyukan da zasu kusanta mu gareka, ka gafarta mana zunubanmu kuma kayi mana kyakkyawan sakamako Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user