Thursday 9 April 2020

Labari Mai Tsuma Zuciya Na Wata Mata Mai Wulakanta Abinci

Tura Wannan Zuwa Ga
A garin bagadaza an taɓa yin rashin ruwan sama na tsawon kwana 40, manyan-manyan waliyyan Allah kimanin 1,20,000 sukayi ta addu'a amma Allah yaƙi yaye rashin ruwan da suke fama dashi.

Izna Ga Masu Wulakanta Ragowar Abinci..

Marubuci:- Shafi'u Dan Gatan Annabi

Ana cikin haka sai wani Bawan Allah Ya shiga halwa yayi ta ibada, yana fitowa yace za ayi ruwa amma ku biyoni ku rakani wani waje.

Bayan sun je dai-dai wani gida sai ya tsaya, yace ayi masa sallama da matar gidan, bayan ta fito yace Baiwar Allah ke ce kika zama sanadiyyar da Allah ya hana mu ruwa tsawon kwana 40.

Tace me nayi ?

Yace kin katsewa ɗanki kashi da gutseren gurasa, sai Allah ya hanamu ruwa saboda an wulaƙanta ni'imarsa ta gutsiren gurasa. Yace yadda za ayi, nuna mana jujin da kika jefar da'ita, bayan sunje jujin suka samu ɓallin gurasar, ya umarceta da ta cinyeta, daga nan Allah ya ci-gaba da ruwa har tsawon sati ɗaya ba ɗaukewa.

Amma a wannan zamanin namu ga Almajiri ma baza'a bashi ba sai a watsar da abincin, shiyasa Allah ke ɗauke ni'imarsa akan mu, bayan Annabi ﷺ Yace ko loma idan ta faɗi ƙasa kada a barta a hadithin Muslim na  2033.

ALLAH YA BAMU IKON KIYAYEWA DAN HASKEN FARAUTAN MANZON ALLAH (ﷺ) AMIN.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user