Friday 17 April 2020

Shin Ko Kasan Kana Yin Rayuwa Da Mutane Hudu Ne A Rayuwar Ka?

Tura Wannan Zuwa Ga
A 'yan shekarun da nake dasu a duniya, nayi mu'amala da mutane iri-iri, na ɗauki darasi da dama.

Rayuwar Duniya Darasi Ce

Marubuci:- Imam Aliyu Indabawa

Wani abu dana karanta game da ɗabi'un mutane ta fuskar mu'amala shine: mutane iri huɗu ne, gasu nan zan bayyana a falsafance.

1. Akwai mutumin da yake kirki amma bashi da mutunci.

2. Akwai wanda ke da mutunci bashi da kirki

3. Akwai wanda yake da kirki da mutunci duk biyun.

4. Akwai wanda bashi da kirki ba shi kuma da mutunci.

Bari nayi sharhin bayanin a taƙaice:

1. Mutumin da yake da kirki bashi da mutunci shine wanda a koda yaushe kuka haɗu zai dinga maka faran-faran yana janka jikinsa, amma babu kalar zagin da bazai maka ba a bayan idonka, shine idan mu'amala ta haɗaku zai yi maka cutar da baka taɓa tsammani ba, irin waɗannan mutane akwai ƙarya, yaudara, cin amana, butulci, hassada da rashin cika alƙawari a tattare dasu.

2. Mutumin da bashi da kirki amma yana da mutunci, shine sau tari ake ganin fuskarsu babu walwala, idan kun haɗu bai damu da yayi maka magana ba, amma fa bazai taɓa zaginka a bayan idonka ba, kuma idan mu'amala ta haɗaku dashi zai kyautata maka fiye da yadda kake tsammani, kayi ta mamaki ashe dama wane yana da mutunci? Irin haka yana faruwa a rayuwa.

3. Shi kuma wanda yake da kirki da mutunci akan same shi da faran-faran da mutane, bazai taɓa cutar dakai a bayan idonka ba, idan mu'amala ta haɗaku zai kyautata maka iyakar iyawarsa, sai dai ajizantaka.

4. Wanda bashi da kirki ba mutunci, shine wanda bai da faran-faran wa jama'a, mai raina mutane, wanda sam bai iya magana ba, mutakabbiri, mahassadi, macuci, ɗan son zuciya, wanda kowa yayi mu'amala dashi sai ya cutar dashi, akwai ire-irensu a rayuwar nan amma 'yan ƙalilan ne.

Yi ƙoƙari ka kyautatawa kowa daga kan fuska har cikin zuciya, domin babu wanda yasan inda rana zata faɗi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user