Friday 8 May 2020

Kalli Hotunan Na'urorin Da Masarautar Saudiyya Ta Samar Yayin Shiga Masallacin Makkah Da Madinah

Tura Wannan Zuwa
Cikin shirye-shiryen buɗe masallacin Harami (Ka'abah) da na Madinah wanda Masarautar Sarki Salman take kan yi, a yau an kafa wasu sababbin ƙofofin a mashigar masallacin Makkah dana Madinah.

Sarki Salman

Marubuci:- Abdulhadi Isah Ibrahim

Waɗannan ƙofofin da suke ɗauke da na'ura mai ƙwaƙwalwa (Computer) da kuma glass zasu bayyana cutar Sarƙewar Numfashi (Corona-Virus) idan mutum yana ɗauke da ita, sannan ƙofofin zasu iya gano duk wata cuta mai yaɗuwa ta iska, idan ƙofar ta gano mutum yana ɗauke da cuta musamman ta corona ba zata buɗe masa ba.

Don daƙile yaɗuwar Covid-19

Sannan ƙofofin suna iya gane idan akwai makami ko wani ƙarfe a jikin mutum.

Don daƙile yaɗuwar Covid-19

Masarautar Sarki Salman na Saudiyya tace waɗannan ƙofofin ba sune asalin waɗanda suke buƙata ba, waɗanda suke buƙata ba'a kammala ƙerawa ba, dazaran an kammala zasu cire waɗannan ɗin su saka wanda suke so ɗin.

Ƙarin hotuna:

Don daƙile yaɗuwar Covid-19

Don daƙile yaɗuwar Covid-19

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user