Friday 19 June 2020

Karanta Nasihohi 10 Ga Dan Uwa Musulmi

Tura Wannan Zuwa Ga
1. KA KULA DA SALLAH: Idan ka ji mai kiran sallah yana kiran sallah ka faɗi irin abin da yake faɗa, ka kyautata alwalarka ka tafi masallaci, ka yi ƙoƙarin tsayuwa a sahun farko, sannan ka tsaya a wurin da kayi Sallah ka karanta:

NASIHOHI GA DAN UWANA MUSULMI

MarubuciAbbati Mai Shago Flg

A. Astagfirullah 3; أَسْـتَغْفِرُ الله (ثَلاثاً)

B. Allahumma antas-salam waminkas-salam, tabarakta ya zal-jalali wal-ikram.; اللّهُمَّ أَنْتَ السَّلامُ، وَمِنْكَ السَّلامُ، تَبارَكْتَ يَا ذَا الْجَلاَلِ وَالإِكْرَامِ.

C. Subhanal-lah walhamdu lillah, wallahu akbar (33). La ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lahu, lahul-mulku walahul-hamdu, wahuwa 'ala kulli shay'in qadir; سُبْحَانَ اللهِ، وَالْحَمْدُ ِللهِ، وَاللهُ أكْبَرْ. (ثلاثاً وثلاثين) لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ.

D. Ka karanta waɗannan surorin tun daga farko har zuwa ƙarshe sau ɗai-ɗai bayan sallar azahar, la'asar da isha'i; suratul ahad (قل هو الله أحد), suratul falak (قل أعوذ برب الفلق) da suratun nas(قل أعوذ برب الناس), sannan sau uku-uku bayan sallar magriba da asuba.

2. KA YI WA IYAYENKA BIYAYYA: Ka yi musu biyayya a kan duk abin da suka umurce ka da wanka suka hane ka in ban da na saɓon Allah, kada ka yi wani abu da zai sa su ce "Tir da kai", ka taimaka musu a kan ayyukan da suka sanya a gaba, in masu ayyukan gona ne ka je ka taya su aikin da kanka ko ka ɗauki nauyin ma'aikaci ya yi musu, in 'yan kasuwa ne ka taya su kula da harkokin kasuwancinsu kuma kada ka ɗauki wani abu ba tare da saninsu ba.

3. KADA KA ZAMA MAROWACI: Rowa aba ce marar kyau, saboda haka ka zama mai bayarwa domin kuwa hannu mai bayarwa shi ya fi alheri fiye da hannun da yake karɓa, ana gane wane yana buƙatar kaza koda bai bayyana buƙatar ba, to ka taimaka masa kafin ya bayyana buƙatar, in kuwa ya bayyana buƙatar ka biya masa ita in kana da iko, ban da faɗar zantukan ɓatanci ko zagi ga wanda ya zo neman taimako wajenka, in ba ka da abin da ya zo nema wajenka ka faɗa masa zance mai daɗi.

4. BAN DA HA'INCI: Ka ji tsoron Allah ka tsaya ka kulawa mutumin da ya ɗauko ka ya ɗora ka a kan kasuwancinsa dukiyarsa, kada ka biya wata buƙata taka ba tare da izininsa ba, idan fa kuka yi yarjejeniya a kan abin da zai riƙa biyan ka duk wata ko wani lokaci sai ka ɗauki kuɗinsa ka biya wata buƙata ba tare da saninsa ba za ka ka biya shi ranar lahira, kai koda ba ku yi yarjejeniya ba ka sanar da shi abin da kake buƙata.

5. KADA KA ZAGI KOWA: Idan wani ya zage ka ko ya yi maka wauta ka kawar da kai daga gare shi, ka nuna ba ta tashi kake yi ba, kuma in wani ya faɗa maka mummunar magana wacce ta ɓata maka rai kada ka tanka masa, ka yi haƙuri, ka yi ƙoƙarin zama ɗaya daga cikin bayin Allah mai rahma, su ne suke tafiya cikin kwanciyar hankali da natsuwa, kuma idan jahilai suka zage su sai su ce a zauna lafiya.

6. KADA KA YI WA WANI ABINDA BA KA SO A YI MAKA: Ka kiyayi cutar da mutane ta kowani ɓangare, kamar yadda ba ka so a yi maka wani abu haka ma sauran mutane ba sa so, ka nisanci abin hanun mutane sai mutanen su so ka, ka kuma amfanar da mutane ta dukkanin fannin da Allah ya hore maka na ilmi ko abin dukiya.

7. KA NEMI ILIMI: Da ilimi ake samun duk wani abin more rayuwa na Duniya da na Lahira matuƙar an yi amfani da shi ta hanya mai kyau, kar ka zama ɗaya daga cikin waɗanda suke zuwa wajen malamai neman ilimi daga baya su dena zuwa ba tare da wani ƙwakƙwaran dalili ba. Wajibi ne dai a kanka ka zama mai ingantacciyar aƙida, sannan ka san Sallah, Azumi, Zakka da Hajji.

8. KA GIRMAMA NA GABA DA KAI: Ka zama mai biyayya ga na gaba da kai, ban da wulaƙanta shi da ƙin bin abin da ya faɗa maka na alheri, in ka ga wani ya taho da kaya ka taimaka masa in yana buƙatar taimakon koda kuwa bai ce "Wane taimaka min ba".

9. KA TAUSAYAWA NA KASA DA KAI: Yara na son kyautatawa, ba sa son matsawa ko takurawa, ka koyar da su ababen alheri cikin hikima da fasaha, ka riƙa musu kyaututtuka gwargwadon ikonka, ban da zaginsu domin kuwa riƙewa suke yi, ka ga ke nan za su iya zagar wani in ya yi musu laifi ko in suna wasa.

10. KA YI GYARA TA HANYA MAI KYAU: Kyautata harshe a lokacin da za ka yi wa wani gyara a kan kuskuren da ya yi ko laifin da ya aikata wajibi ne a kanka, Allah ya koyar da mu yadda za mu yi gyara, ga umurnin da ya ba mu "Ka yi kira zuwa ga hanyar  Ubangijinka da hikima da kyakkyawan wa'azi..."  babu zagi ballanata wani abu mai kama da shi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tushe/Asali: www.muryarhausa24.com.ng
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user