Friday 31 July 2020

Haduwar Sallar Idi Da Sallar Juma'a A Rana Daya Mene Ne Abin Yi?

Tura Wannan Zuwa Ga
In aka dubi hadisai da atharan da suka zo akan wannan mas'ala, da kuma tattaunawar da malaman fiqhu da hadisi suka yi akai.

HADUWAR IDI DA JUMA'A A RANA ƊAYA..

Marubuci:- Dr. Kabir Asgar

Za a iya fita da sakamakon da ke biye:

1. Wanda ya sami sallar idi an yi masa rangwamen wajabcin halartar sallar Juma'a a wannan rana, sai dai zai sallaci azahar don hakan shine asali ga wanda Juma'a ta faɗi a kan sa, amma da zai ɗauki azeemah ya je Sallar Juma'ar to da ya fi falala.

2. Wanda bai halarci idi ba to wannan rangwamen bai hau kansa ba, don haka Juma'a na nan a kansa a matsayin wajibi matuƙar ba shi da wani uzuri yardajje a Shari'a.

3. Wajibi ne akan limamin Juma'a ya tsai da Sallar Juma'a don waɗanda ta wajaba a kansu su samu halin sauke ta da su da waɗanda ke fatan samun falala biyu.

4. Ba a shar'anta Kiran Sallar Azahar a wannan rana, haka nan ma tsai da jam'inta a masallatan da ba na Juma'a ba, abin da ya fi shine wanda ba su je Juma'a ba su sallaci azahar ɗin su daidaiwa.

5. Zancen da ke cewa wanda ya halarci idi ba sai ya yi Sallar Juma'a ba, kuma ba zai yi azahar ba, zance ne maras inganci, saboda haka ne ma malamai suka tunkuɗe shi, suka ce kuskure ne, suka kuma baiwa waɗanda sukai fatawa da shi uzirin cewa, mai yiwuwa atharan da ke nuna cewa magabata suna yin azahar ɗin ba su riski waɗannan malaman ba ne.

Allah Ubangiji shine mafi sani, Allah Ubangiji ya sa mu dace Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user