Tuesday 6 October 2020

Shin Ko Kasan Irin Matsayin Da Kake Da Shi A Cikin Al'umma?

Tura Wannan Zuwa Ga
Ana so a rayuwa ka yi ƙoƙari ka zama ƙofa wadda Alkhairi yake shigo ma mutane daga cikinta. Idan ka kasa yin hakan to, ka zama taga ana samun haske daga wurinka. Idan bai yiwu ba, sai ka zama bango wanda ake jingina gare shi.

YAYA KAKE A CIKIN AL'UMMA...

MarubuciSheikh Aliyu Sa'id Gamawa

Kada ka yarda ka zama kamar shanyayyen hannu a cikin al'ummah wato mai rauni maras amfani sai ɓata kama da nuna tawaya.

Kuma kada ka zamo mai buɗe ƙofar sharri ko jawo fitina da yaɗa ɓarna ga al'umma. Haka nan kada ka zamo laruri kuma nauyi da matsala ga mutane.

Mafi Alkhairi daga cikin mutane shine wanda mutane suke amfana da shi. kuma ka zamo kamar zaure ɗakin fakewa, ko bango abin jingina, ko damina uwar albarka.

Allah ya rufa mana asiri ya tsare mana imanin mu da mutumcin mu yasa mu gama lafiya, Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user