Sunday 29 November 2020

Kalli Kyawawan Hotunan Kafin Aure Na Jarumi Nuhu Abdullahi Da Amaryar Sa

Tura Wannan Zuwa Ga

Kamar yadda shafin
MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin hotuna masu inganci waɗanda suka fi ɗaukar hankulan shafukan sada zumunta.

Kafin Aure

MURYAR HAUSA24 Yau ma gamu tafe da hotunan kafin aure na fitaccen jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood) Nuhu Abdullahi.


Katin Gayyata


Jarumi Nuhu Abdullahi zai angwance a ranar huɗu ga watan disamba na shekarar dubu biyu da ashirin (4/12/2020), wanda za'a ɗaura auren da misalin ƙarfe ɗaya da rabi na rana (01:30 pm).


Amarya da Ango

Hotunan sun ɗauki hankula sosai a shafukan sada Zumunta duba da yanayin da aka ɗauki hotunan, wanda hakan ya taka muhimmiyar  rawa sosai wajen ƙayatar da al'umma daga sassa daban-daban na faɗin ƙasar dama Duniya baki ɗaya.


Kafin Aure


Jarumi Nuhu Abdullahi zai angwance da kyakkyawar amaryarsa Jamila Abdulnasir wacce aka yiwa laƙabi da Siyama.

Amarya da Ango

Nuhu Abdullahi ɗaya ne daga cikin jaruman da suke fitowa a fina-finan turanci baya ga fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood.

Kafin Aure

Ɗaya daga cikin fina-finan turancin da ya fi shahara a fim ɗinsa shine There is a Way , wannan shiri ne wanda ya samu kyakkyawan aiki da kuma fitattun jarumai masu ruwa da tsaki a al'amuran Kannywood.

Amarya da Ango

Idan mai karatu bai manta ba, jarumi Nuhu Abdullahi ya kasance ɗaya daga cikin fitattun jaruman shirin Labarina, wanda ake haskawa a tashar AREWA24, rawar da yake takawa a cikin shirin Labarina a matsayin saurayi mai kwaɗayin abin duniya da ƙoƙarin cimma burin sa na zama tauraro a duniya, yasa ya rabu da Sumayya, duk da cewa, yasan tana matsanancin ciwon Son shi, amma yayi fatali da Soyayyar ta don cimma burin shi.

Kafin Aure

Kalli ƙarin wasu hotunan a ƙasa:


Amarya da Ango

Kafin Aure

Amarya da Ango

Kafin Aure

Amarya da Ango

Kafin Aure

Amarya da Ango

Kafin Aure

Amarya da Ango

Kafin Aure

Amarya da Ango

Kafin Aure

Ku Ci gaba da kasancewa da Mu domin samun Cikakken Tarihin Nuhu Abdullahi nan bada daɗewa ba Insha Allah.

Amarya da Ango

MURYAR HAUSA24 Muna yi Musu fatan alkhairi.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user