Friday 1 January 2021

Karanta Zafafan Sakonnin Soyayya Na Barka Da Rana Masu Ratsa Zukatan Masoya

Tura Wannan Zuwa Ga

KI AMINTA DA BATUN SOYAYYA TA


Na daɗe ina son Ki a cikin zuciya ta tun kafin na yanke shawarar furta miki hakan, ki aminta da batun soyayya ta a gare ki, ki amince mu gina rayuwa mai inganci, ki zamo tawa ni ma in zamo naki, wannan shi ne burin zuciya ta, ki amince da ni a matsayin wanda za ki rayu tare da shi har abada, zan yi ƙoƙarin samar miki da farin ciki mai ɗorewa. Ina Son Ki.



Rubutaccen Saƙon Soyayya



MarubuciAbba Muhammad Dan Hausa



FATA NA


Ko da a ce na mutu na bar duniya ba tare da buri na ya cika na zamowa ango a gare ki ba, ina fatan ki zamo mata a gare ni a cikin Aljanna mu rayu a tare na tsawan lokacin da bashi da iyaka. 


MURMUSHIN KI NA KORE MIN ƘISHI


A dukkan lokacin da na ji muryarki, ta kan zamto wani mashari da ke share damuwar dika zuciya ta, ganin murmushinki na haskaka idanuwa na, kalaman bakinki na kore min ƙishirwa, haɗuwa ta da ke ya sanya rayuwa ta, ta cika da farin ciki. Ina Son Ki. Ki Huta Lafiya.


SAMUN FARIN CIKIN KI SHI NE BURI NA


Buri na a kullum na ji muryarki, hakan ya sa nake matsawa wajen kiran lambar wayarki, ina fatan bana takura miki a bisa hakan? Domin kuwa samun farin cikinki shi ne muradi na.


INA SON KI SO MARA MISALTUWA


A dukkan lokacin da na rasa ki, zan kasance cikin ciwo da ƙunar zuciya, zan samu sassauci ne kawai a lokacin da na ga giftawarki a mafarki ko a zahiri, ina son ki so mara misaltuwa. Ke ce hasken idaniya ta. Ki huta lafiya.


INA FATAN DAWWAMAR FARIN CIKIN KI


Ba zan iya jure tsayawa kallon kwaranyar hawaye daga cikin idanuwan kowace mace ba, hakan ya sa zan iya yin komai domin ganin cewa hawayenki bai zuba daga cikin idanuwanki ba, idan kuma har ya zuba zan hanzarta tsayar da shi cikin gaggawa. Ina fatan dawwamar farin ciki a zuciyarki. Ina Son Ki.


FATA NA, MU RAYU TARE


Ina jin wani abu a cikin zuciya ta a kanki, na san ba zai wuce tsiron sonki ba, ina fatan na mallake ki, ki zamo tawa har abada, idan har kika nesanta da ni, tabbas rayuwa ta za ta shiga garari, da ke nake fatan mu rayu tare a matsayin mata da miji na tsawan rayuwa. Ina Son Ki.


ABAR SON KALLON IDANIYA TA


Rashinki a kusa da ni na sanya wa a lokuta da yawa na ji na tsinci kai na cikin kaɗaici, da jin tamkar ni kaɗai ke rayuwa a duniya, ko da kuwa a ce ina cikin taron jama'a ne, ina cike da kewar rashin ganin tattausan murmushinki da fararen idanuwanki, a kullum begenki na linkuwa a cikin zuciya ta. Ke ce abar son kallon idaniya ta. Ina Son Ki.


KI AMINTA DA NI


Da ganinki zuciya ta, ta aminta da ke hakan ya sanya ta yi min jagoranci izuwa gare ki, zan so ta ki zuciyar ta aminta da ni ta yadda za mu zama aminan juna, ko da a ce kowa ya yi nesa da ke ni kuma zan kasance a tare da ke har abada, taimaka ki sama min gurbi a cikin zuciyarki, domin zama ɗaya daga cikin tarin masoyan da suke kewaye da ke. Ina Son Ki.


SON KI YA GAME JINI NA


A iya sani na masoyi na gaskiya shi ke sanin halin da masoyiyarsa ke ciki ko da kuwa ba ta furta masa hakan ba, na kan kasance cikin irin yanayin da kike ciki na farin ciki ko akasin haka, a lokacin da muke tare ko muka yi nesa da juna, son ki ya bi jijiya ya game jini na. Ina Son Ki.


KAR DA KI MANTA DA NI


SO abu ne mai saurin jefa zuciya a damuwa, ya nesanta ta da farin ciki, amma ya kan zamo abu mai daɗi ga dukkan wanda ya samu masoyiya irin ki, karda ki manta da wanda zuciyarsa ta faɗa a sonki na tsawan lokaci, wato ni. Ina Son Ki.


SAMUN SOYAYYAR KI SHI NE MURADIN ZUCIYA TA


Ina son ki zan kuma ci-gaba da son ki na tsawan rayuwa ta, samun soyayyarki shi ne babban muradin zuciya ta. Ginegine na rushewa, mutane na mutuwa, amma soyayyar gaskiya ba ta taɓa gushewa har abada. Ina Son Ki.


ZAN CI-GABA DA BAKI KULAWA


Da a ce da yawan mata haka suke nuna tausayawa ga masoyansu kamar yadda kike yi a kai na, na tabbata da tini baƙin ciki da damuwa sun zama tarihi a duniya. Ina son ki kamar yadda kike so na, zan kuma ci-gaba da baki kulawa.


NA AMINTA DA CEWA KINA SO NA


Mutane na yin mamaki akan yadda sonki yake neman sanya wa na zautu, amma ni sai nake ganin abun da ya kamata su yi mamaki a kansa shi ne, yadda kike nuna kulawarki a kai na. Tabbas, ina son ki, kuma na aminta da ke ma kina so na. Allah ya nuna mana lokacin da za mu zamo mata da miji, shi ne buri na.


INA TARE DA KE A DUK INDA NAKE


A ko da yaushe kina cikin zuciya ta, ko da a ce bacci nake ko a farke. Tafiya nake ko a zaune, kina nan a cikin zuciya ta, ina tare da ke zan kuma ci-gaba da kasancewa a tare da ke a duk inda na tsinci kai na. Ki Huta Lafiya. 


ZUCIYA TA DA KAI TA AMINTA


Shin ka kuwa san wani abu? A duk faɗin duniya babu wani wanda zuciya ta, ta aminta da shi take so irinka, a kullum ina fatan soyayyarmu ta yi nisan da za ta zaga duniya. Ba zan taɓa mantawa da kai ba har abada.


BURI NA MU RAYU A TARE


A kullum Buri na bai wuce na ganin na mallake ka a matsayin miji na uban 'ya'ya na ba, na kasance a tare da kai cikin dare ko rana, da sanyi ko zafi, mu rayu a tare har abada. Ina Son Ka.

 

SON KA NA GIRMA A CIKIN ZUCIYA TA


Sonka ya tsira a cikin zuciya ta, hakan ya sa nake kwana cikin tinaninka, ganin murmushinka da jin muryarka na zama takin dake ƙara wa sonka girma a cikin zuciya ta a kowa ce sa'a. Ka Huta Lafiya.


SAHIBI NA


Kai ne numfashi na, ba zan iya rayuwa ba tare da kai ba. Ina son ka


BA ZAN TAƁA MANTAWA DA KAI BA


Sonka a cikin zuciya ta, ya zamto tamkar wani shukakken fure ne mai tsananin ƙamshi, da kyawun kallo. Sonka ya kasance cikin zuciya ta, ta yadda futarsa zai zama abu mai matukar wahala. Ba zan taɓa mantawa da kai ba a rayuwa ta. Ina son ka.


 SAKO MAI MUHIMMANCI


Kana da damar tura wa abokiyar tsinkar furenka, amma ba a amince wani ya yi amfani da shi da niyyar yaudarar wata ruhi ba. Akwai mai ganin Ka/Ki a ko'ina wato Allah. A kiyaye haƙƙin mallaka, a guje wa satar fasaha.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user