Sunday 30 May 2021

Karanta Sababbin Sakonnin Soyayya Na Barka Da Hutun Karshen Mako

Tura Wannan Zuwa Ga

NA MAZA


HASKE


Ke ce hasken ranar da ke haska min dare na san safiya ta yi a duniyata, ke ce iskar da nake shaƙa domin na rayu, ke tamkar igiyar ruwa ce a cikin kogin da nake ninkaya, ke ce bugun zuciyata da yake bambance rayuwa da mutuwata. Ina Son Ki.


Barka Da Hutun Ƙarshen Mako


MarubuciAbba Muhammad Dan Hausa


MADUBI


Son da nake yi miki tamkar madubi ne a cikin zuciyata. Ko da a ce ya fashe, idan kika sanya idanuwanki a kansa za ki tarar da ke a cikinsa. Son ki ya zamo jini a jikina ya bi ta jijiyoyin jikina ya narke a cikin zuciyata. Ina Son Ki Sarauniyata.


RANA


Ranar da za a ce ga ki a kusa da ni, a wannan ranar zan ji ni a matsayin cikakken mutum mai sa’ar da babu irin sa, a wannan rana zan yi takun ƙasaita tamkar na sarkin da ke da daular da babu irin ta a duniya, saboda na mallaki mai kyawun da babu kamar ta, wadda nake fatan mu rayu tare rayuwa ta har abada. Ina hango mana rayuwa mai tsawo cikin shekaru masu ɗauke da ranaku masu ban mamaki a nan gaba. Ina Son Ki Gimbiyata.


TUNANI


A dukkan lokacin da tunanin kyakkyawar fuskarki ya bujuro a cikin zuciyata, sai na ji zuciyata ta ƙara narkewa a cikin soyayyarki, na ji na kamu da matsanancin begenki, kewarki mara misaltuwa ta dabaibaye ni ta yadda nake kasa tsaida zuciyata daga tunaninki. Ina Son Ki.


AMINTA


A lokacin da taurari suka kasance suna haska saman duniya da haskensu, mu kuma mu kasance tare a ƙasanta muna masu haska cikinta, wannan abu ne da zuciyata tuni ta aminta da shi tare da ƙaguwa wajen ganin mun kasance tare tamkar jini da tsoka, zan so a kullum ke ma kamar ni burin son ganin faruwar hakan ya kasance a cikin zuciyarki. Ina Son Ki. Fatan Kina Nan Lafiya?


MURMUSHI


Macen da murmushinta ke haska duhun dare, macen da sautin muryarta ke sanya nutsuwa a zuciyar mai sauraro. Kin samar da farin ciki a cikin zuciyata, kin zamo mace ɗaya tilo da babu kamar ta a cikin idanuwana. Ina Son Ki.


MACE


Amincin Allah ya tabbata a gare ki, mace ta farko da ganin kyawunta a karon farko ya hana ni bacci a tsawon dare, ya hana ni sukuni a tsawon yini, macen da ta tsaida zuciyata daga tunanin komai sai nata, macen da nake so kuma zan ci gaba da so har ƙarshen rayuwata. Ina Son Ki.


WALWALA


Ke ce babbar kyautar da a tarihin rayuwata na taɓa samu wadda ba zan taɓa mantawa da ita ba. Ina son ki. Ina fatan tabbatuwar murmushi a saman fuskarki tare da kasancewarki cikin walwala da farin ciki a ko da yaushe.


BEGE


A lokacin da na ga hoton kyakkyawar surarki na kan yi murmushi ko da ina cikin damuwa, na kan faɗa cikin tunanin kyawawan idanuwanki da tattausan murmushinki. Ya kan gusar da hankalina daga sauraren komai da tunanin komai sai naki, ya kuma iza wutar begenki a cikin zuciyata. Ina son ki masoyiyata, abar tunanina.


MAFARKI


Ke ce mai ƙawata baccina a duk cikin dare, a lokacin da kike bayyana a cikin mafarkina kina mai haske ni da hasken murmushinki mai taushi. Zan so ki kasance a tare da ni a rayuwarmu ta zahiri kamar haka..., na tabbata jama’a zasu koma kirana da Yarima ko Ɗangata, saboda na mallake ki. Ina son ki.


SO


Son da kike yi min, shi ne abu mafi girman dukkan wata kyauta da na taɓa samu a rayuwata. Kamar yadda na sha sanar da ke a baya ina son ki, so mara iyaka, wanda bai da lokacin yankewa. Ki kula min da kanki.


ZAƁI


Ba na yin nadama ko da-na-sani da zaɓenki a matsayin masoyiyata, saboda ke ce zaɓin raina kuma ke ce mahaɗin rayuwata, ke ce wadda na jima ina nema. Fatana na rayu tare da ke a matsayin uwar ‘ya’yana, na kuma mutu ina mai fatan sake haɗuwa da ke a gida mafi soyuwa ga kowane mutum wato Aljanna. Ina Son Ki.


MURYA


Barka da safiya masoyiyata, kyakkyawar macen da babu kamar ta, mai sanyin muryar da ta zarce sarewa, mai kyawun ido da kyawun kallo, ina fatan kin tashi lafiya kyakkyawar zinariyata?


TAMBAYA


Son ki ya shiga zuciyata ta yadda ba zan iya wuni ba tare da tunaninki ba. Yadda nake ji a cikin zuciyata a kanki ya sanya ni jin cewa ina son ki ne fiye da yadda kowa yake nuna hakan a kanki. Idan har kika tambaye ni mai ya sa, ba zan iya sanar da ke dalili ba. Zan ci gaba da son ki har na tsawan rayuwata, zan kasance a tare da ke ba zan bari ki kuɓuce min ba. Ke tawa ce ni naki ne, fatan za ki amince mu rayu tare rayuwa ta har abada? Ina Son Ki.


NUMFASHI


Son ki na bayyana kullum a cikin zuciyata, tamkar yadda rana ke futowa a sararin samaniya, ya yaɗu a cikinta ya ƙawata ta, fiye da yadda taurari ke ƙawata sararin samaniya a cikin dare. Ina son ki kuma zan ci-gaba da son ki har zuwa fitar numfashina.


NA MATA


SIRRI


Ba kowa ba ne ake faɗa wa sirrin zuciya sai mai cikar matsayi da cancanta kuma wanda ya dace. Babu komai a cikin tawa zuciyar sai kai da tunaninka. Ina Son Ka.


TAFIYA


Fatana a ko da yaushe na kasance a kusa da kai, na kasance cikin fara’a domin ka, ko da tafiya nake ya kasance kana kusa da ni, ko da magana zan yi ya kasance kai ne mai amsa tambayata. Ina son ka so mara iyaka da lokacin ƙarewa Yarimana. Ka Huta Lafiya.


AIKI


Ganin ka a cikin baccina, na ɗaukaka dukkan daren da na yi mafarkinka a cikinsa, fiye da sauran dararen da babu kai a cikinsu. Tunaninka ya na sanya ni murmushi. Kasancewa a tare da kai, shi ne mafarkin da nake fatan ya tabbata a zahiri. Son ka shi ne aikin da zuciyata za ta kasance cikin yi a tsawon rayuwata. Ina Son Ka.


BUƘATA


Ina son kasancewa a tare da kai na tsawan rayuwata, fiye da yadda mai tafiya ke bukatar ruwa a tsakiyar sahara, fiye da yadda gangar jiki mai numfashi ke buƙatar iska, fiye da yadda tsirrai ke buƙatar hasken rana. Ina son ka tun daga babin farko na labarin rayuwata har izuwa ƙarshe. Ina son ka Yarimana.


ƊAYA


Da za a raba kaina gida biyu a taradda ƙwaƙwalwata na san babu abin da za a tarar a ciki sai tarin tunaninka. Da za a buɗe ƙirjina a taradda zuciyata na san babu komai a ciki sai ajiyarka. Da za a tsaga fatar jikina jini ya fita na san tabbas sai an ga naka. Mun zama ɗaya, kuma ina fatan mu kasance a wuri ɗaya na har abada.


KEWA


Kai tamkar fure kake mai kyawu da ƙamshin da babu kamar sa. A dukkan lokacin da ban ji muryarka ba ko ban ga hoton kyakkyawar fuskarka ba na kan kasance cikin kewarka. Kai na musamman ne a gare ni. Ina Son Ka.


ALFARMA


Da za a hana ni ci da sha, sannan a killace ni wuri ɗaya, amma a yi min alfarmar jin muryarka, da ni kuwa na yi ikirarin na fi kowa gata a duniya. Sautin muryarka tattare yake da sirrin ci da shana da duk farin cikina. Ina alfahari da kai.


SAKO MAI MUHIMMANCI


Kana da damar tura wa abokiyar tsinkar furenka, amma ba a amince wani ya yi amfani da shi da niyyar yaudarar wata ruhi ba. Akwai mai ganin Ka/Ki a ko'ina wato Allah. A kiyaye haƙƙin mallaka, a guje wa satar fasaha.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user