Tuesday 25 May 2021

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (34) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga

BAMBANCIN HANZARI DA GAGGAWA


Hanzari yana nufin ka ƙara saurin tafiyarka ne don ka isa zuwa ga nasara a dai-dai lokacin da ake buƙatarka, gaggawa kuwa na nufin ka yi saurin aikata abu tun lokacin aikin bai yi ba, kenan hanzari ake buƙata ga mai son cin nasara ba gaggawa ba, domin abinda ake so shi ne mutum ya iya samun abinda yake buƙata da surar da yake buƙata ɗin, mun taɓa zuwa tambayar wani karatu na NCE sai aka ce mana akwai "regular" shekara uku, part time shekara huɗu sai kuma long vacation shekara biyar, in mutum zai iya sai ya ɗauki ta shekara uku don ya yi hanzari ya gama, in ba zai iya ba kuma ya ɗauka to ya yi gaggawa kenan.


Bambancin Hanzari Da Gaggawa


MarubuciBaban Manar Alkasim


Duk wata sana'a ko aiki da mutum zai yi ya kamata ya tabbatar hanzari zai yi ba gaggawa ba, wata mata da aka kawo mata kishiya sai ta fara nuna wa kishiyar cewa ita keda mijin, tana saka ta ayyuka daban-daban, har amaryar ta goge idanunta ta ce ita ba baiwa ba ce, daga ranar ta daina yin komai, har da wanda ya dace ta yi ɗin ma, ta ce matsayinsu guda ne, na ce gaskiya uwargidan ma ta yi gaggawa, da ta yi haƙuri ta janyo yarinyar a jiki, ta nuna mata abinda ya dace, koda an gaya wa amaryar ƙarya da gaskiya in ba ta ga abinda ake gaya mata ba za ta sauko ta yi abinda ya dace, ba abin da mutum zai bi a hankali sai ya ga ribarsa ko meye kuwa.


Na ga wani mai aski yana ta faɗa, da yake rigimar ba tawa ba ce sai na ja bakina, wai yaron da ya zo koyon aiki ne ya tsaya sai an riƙa raba kuɗin da ya samu kashi biyu ana biyansa, alhali ogan yana ganin yaron ne ma zai riƙa biyan koya masa da ake yi, ni dai ban sa baki ba, amma na san mai koyon aiki a wasu wuraren shi ne ma yake biya ba shi ake biya ba, kamar dai yaron ya yi gaggawa, tunda ba a ce ya biya ba bai dace ya ce a biya shi ba, a ƙarshe dai sun rabu, ina da tabbacin cewa indai yaron zai ci gaba da haka ko ina ya je irin wannan rabuwar za a yi.


Waɗansu sun shirya yin wani kamfani sai suka tara kuɗin farko a hannun ɗaya daga cikinsu, kusan shi ake so ma ya riƙa ajiye kuɗin, a ƙarshe dai wannan kuɗin bai fito ba, sai a albashinsa aka riƙa cirewa a hankali, kuma an amshe tarin daga hannunsa, saboda bayyanar rashin gaskiya ƙiri-ƙiri, na ce ya yi gaggawa ne, da ya yi haƙuri akwai wasu kuɗi na masamman da ake bai wa duk mai tarin kuɗi, da ya rabauta da shi, wanda ya fi ba ni mamaki shi ne wanda ya je neman auren wata yarinya, an ba shi ita kuma an saka masa rana, sai da ya rage saura 'yan kwanaki kaɗan sai ta yi maganar kayan ɗaki ya ce yana da wani ƙwararren kafinta.


Ashe gogan naka ya bi ta kan kuɗin ne, auren da bai ɗauru ba kenan, sai gashi ana ta wasan kurar boyo tsakaninsa da amaryar, gaskiya ya yi gaggawa, da ya bari ya aure ta tukun, komai nata inda soyayya nasa ne, gajin haƙuri ne, wata kuma maigidanta ne ya auro ƙawarta ba tare da saninta ba, ya ce in ta sani za ta iya dagula lamarin, a taƙaice dai ba ta sani ɗin ba sai bayan an ɗaura, nan fa uwargidan ta tada bala'i har ya kai ga ta bar wa amaryar mijin, da ɗakinta da ma yaran da ta haifa, saboda kishi, na ce ta yi gaggawa, da za ta bi a hankali da ta riƙe kayanta gaba ɗaya.


Akan yi gwaji ne don tabbatar da ko mutum zai yi gaggawa, duk da cewa ina tababar maganar gwaji a neman aure, wasu matan sukan yi asarar miji na gari a dalilin gwaji, na tabbata ba shi ne hanya ta ƙwarai wurin zaɓin miji na gari ba, don da shi ɗin ne da Annabi (S.A.W) ya zaɓar mana, amma bincike shari'a ta tabbatar, in dai namiji ne to mace ta bar shi da kininsa kawai, maƙwabta abokan aiki, 'yan uwa duk za su iya taimakawa wurin bincike, kuma su ɗin ne za su kawo abinda ya dace.


Wani ɗan abu ne ya shiga tsakaninsu ita kuma ta nemi saki a matsayinta na mace, gaulan naka ya ba ta duk da cewa namiji ne, a kullum suna tare, bayan ba aure a tsakaninsu, sai ya zamanto duk bayan 'yan kwana biyu sai ta ɗauko yaro ta zo gidansa wai ta kawo masa ɗansa ya gani, amma sai su kwashe sa'o'i biyu zuwa uku bai gama ganin yaron ba, na ce sun yi gaggawa, da sun yi haƙuri za su fahimci junansu, haka dai suka ci gaba har wanda tsautsayi ya faɗa masa ya aure ta, ba ta jima ta fice abinta ta koma inda ta fito.


DUBA WANNANKaranta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (35) Cikin Sauki


Wasu kuma duk an yanke musu hukunci mai tsanani akan kashe wani da suke zargin cewa ya kashe musu ƙani, alal aƙalla da sun danƙa shi a hannun hukuma, a tunanina ba mutumin da zai wuce kwanakin da Allah (SWT) ya ɗiba masa, matuƙar dai za su iya kashe shi a wannan lokacin to sun yi gaggawa, domin ko ba su taɓe shi ba mutuwa zai yi, akwai abubuwa da dama da muke rasawa a dalilin gaggawa irin wannan, ba laifi ba ne su yi hanzarin miƙa maganar kotu kafin bincike ya kai gare shi, amma kashe shi kam gaggawa ne.


Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user