Sunday 13 June 2021

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (35) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga

ƘANANAN MATSALOLI


Akwai ƙananan matsaloli da sukan faru nan da can, in mutum ya haɗu da matsala a wurin aikinsa, kamar a kan kayan sana'ar, ko tsakaninsa da maigidansa, ko abokan aiki, lallai ya yi ƙoƙarin gyarawa kar ya bari lamarin ya yi girma yadda zai shiga cikin matsalar da a ƙarshe ya kasa fitar da kansa a ciki. Misali: ɗaliba ce ta faɗi mummunar magana game da malaminta, ba a gabansa ta faɗa ba, sai wasu ƙawayenta suka ɗauko suka gaya masa, wannan matsala ce mai sauƙi, duk da cewa ransa zai ɓaci amma ya kamata ya mu'amalanci lamarin da hikima.


Ƙananan Matsaloli

MarubuciBaban Manar Alkasim


Ba a gabansa ta faɗa ba, ya bari sai ta faɗi a gabansa ɗin sai ya ɗauki matakin kaiwa gaba, wani da irin wannan ya faru sai ya sa aka yi masa kiran ɗalibar ya zazzage ta a ƙarshe ya mare ta yadda ta ji jiki, a gaban ƙawayenta, wannan ya sa ta ji zafi da ta bar wurin ta bankaɗo wani sirrin da hakan ya gigita shi, mai makon ya ɗauki darasi a kan abinda ya faru a baya sai ya same ta ya yi mata dukan tsiya, duk jikinta ya kumbura, yarinya ta kai ƙara wurin uwayenta, su kuma suka bi kadin magana, a ƙarshe aka ƙare a kotu.


Ashe dai malam ya ɗan zazzagaya yarinya, shi ya sa ba ta ganin girmansa ko-kaɗan lokacin da ya yi mata ba daidai ba ta ɗan ladabta shi, wajen ƙoƙarin nuna mata cewa ba ta isa ba allura ta tono garma, makaranta ta kore shi, kotu ta ɗaure shi, gashi kuma ya riga ya ɓata sana'arsa gaba-ɗaya, yanzu ko ya fito ba kowace makaranta za ta ɗauke shi ba, ba wai bai da abinda zai bayar ba ne, uwayen yaran ne za su ji wa 'ya'yansu tsoro, dole dai makaranta ta dakatar da shi, samun aiki kuma a wani wurin sai ya yi babbar sa'a, to ina nasarar da aka ci?


Akwai wata mata da take zaune a gidan aurenta, a kullum tunaninta ɗaya wato abokiyar zamanta, ba za ka taɓa jin wata magana mai daɗi a bakinta dangane da wancan ba, har dai ɗayar ta samu labari ta biyo ta jin ba'asin irin maganganun da take faɗi game da ita, kamata ya yi ta yi amfani da ƙwaƙwalwa wurin warware matsalolinta, amma sai ta ƙi, a ƙarshe suka ɗaga harshe har ta kai ga ta zargi kishiyar da karuwanci kafin maigidanta ya aure ta, ashe ita ma kishiyar tana da nata sirrin, nan fa ita ma ta ce "Na gode Allah tunda kafin aure ne na yi, kuma na tuba ina fatan Allah ya yafe min, ke ba wane yake ɗibarki har yanzu ba ko kina zaton ba mu sani ba ne?"


Magana kamar wasa ta nemi ta zama yaƙin badar, don an shigo da maƙwabci cikin rigima, musamman yadda ɗanta ƙarami ya yi kama da shi sosai, kama kuwa ba 'yar ƙarama ba, a taƙaice dai tana gidansu auren zai ɓaci, abin takaici ma makomar yaron da suke ƙoƙarin saka shi a halin ha'ula'i, kai da sauran yaran ma guda biyu, maganar gaskiya ba wata nasarar da ta ci ta zama a gidan aurenta, don an kaɗa ta waje, 'ya'yan da ta haifa ma ana tababan na gida ne ko kawo su aka yi daga maƙwabta, asali wannan matsalar da ta bi ta a hankali da ta warware ta cikin sauƙi, yanzu ga ƙilu ta jawo balau.


A duk lokacin da matsala ta zo maka matuƙar ba ka son ta to kawar da ita, kar ka yarda ta ƙara girma bare ta fasu zuwa gida biyu ko uku, ko mutum guda kake da matsala da shi a wurin aiki yi ƙoƙari ku daidaita, kar ka yarda ya samu wanda zai goya masa baya su zama su biyu a kanka, yin hakan zai taimake ka wurin kaiwa ga nasara ba tare da ka ji jiki ba, ba yadda za a yi mutum ya rayu a wuri ba tare da matsaloli ba, sai dai wasu su na da dabarun taka wa matsalolinsu ne burki wasu kuma sukan bar su ne har su shanye su, a ƙarshe a koma gidan jiya.


Da farko in akwai matsaloli a gabanka kar ka yi musu kuɗin goro, bi kowanne ka warware shi cikin sauƙi, wani kuɗi yake buƙata, wani ban haƙuri, wani bai buƙatar ka je masa kai tsaye sai ka nemi taimakon mai shiga tsakani, zai yi kyau ka iyakance kowace iriyar matsala, maibuƙatar ban haƙuri ko kai ke da gaskiya same shi ka ba shi haƙuri a wuce wurin, ka dai rufe bakin tsanya, wanda yake binka bashi yi ƙoƙari ka biya shi, ko ka gamsar da shi, gobe in ka nema zai ba ka, in ka ɓata masa rai daga lokacin an gama kenan, ba zai ƙara ba ka ba.


Wanda ka ga zama da shi ba zai taɓa yuwuwa ba yi ƙoƙari ka guje masa gaba ɗaya, in kuma dole sai an zauna a wurin to ka yi ƙoƙari wasu su san irin zaman doya da manjan da kuke yi, kuma ka nemi su yi muku sulhu, in ya ƙi to za su kasance tare da kai, ko ya so yi maka sharri za su taimake ka don sun san matsalar, in ka fahimci cewa mayar da bashi yana yi maka wahala to kar ka karɓa, in ma ya zama dole to ka san irin waɗanda za ka karɓa a wurinsu, da gwargwadon da za ka karɓa ɗin, in ana zarginka da wani abu kar kullum ka tsaya kan cewa ba ka da shi, yi ƙoƙari ka yi maganinsa.


DUBA WANNANKaranta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (36) Cikin Sauki


Sannan mai son cin nasara kar ya gina wa kansa kurkuku ya shiga ya kulle kansa, bare a kai ga saɓa wa mahalicci, yadda mutum zai fara gaya wa kansa "To ni ya Allah ya halicce ni haka ne?" Ko "Ya saka ni a wannan matsayin" a kullum ka kalli matsalolinka ka yi ƙoƙarin warware su, in ana zarginka da yawan surutu kar ka ce ba ka da shi, amma ya za a yi ka kawar da abinda ake zarginka da shi? Shin maganar ce ratata, ko ɗaukar maganar wannan da wancan ka faɗi a wasu wuraren, ko ƙarairayi? Duk abubuwa ne masu alaƙa da juna, in ka fahimci kanka za ka iya gyarawa.


Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user