Friday 25 June 2021

Mu Kori Yada Barna

Tura Wannan Zuwa Ga

MUNA CIKIN WATA IRIN AL'UMMA A YAU


Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai


"Yau Allah ya kawo mu cikin wata iriyar al'umma wacce muke rayuwa acikinta, duk nagartarka, duk taka-tsan-tsan ɗinka, dole ne sai kayi musharaka da mutanen banza a rayuwarka, dole sai ka yi mu'amala da su ta kusa ko ta nesa koda baka so hakan ba".


Mu Kori Yaɗa Ɓarna

MarubuciMuhammad Umar Baballe


"Mu'amala ta kusa itace: wataƙila gurin aiki ya haɗaku guri ɗaya da su, kuma kayi-kayi su shiryu amma Allah bazai basu ikon shiryuwa ba, wannan wata babbar jarabawa ce a gare ka".


"Mu'amala ta nesa kuma, za ka dinga jin ambaton su daga gurin wasu makusantan naka ko abokanan zaman ka, nan ma kayi-kayi ka toshe kunnen ka daga barin jinsu, amma hakan ba abu ne mai yiwuwa ba, wannan itama babbar jarabawa ce a rayuwarka".


"Yanzu mu ɗauki batun mawaƙan mu ji, SubhanAllah! Kai ustazu ne, an san dai cikakken ustazu babu abin da zai haɗa shi da sauraron kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe, amma kuma duk ya haddace sunayen mawaƙan garinsu, to menene yake kawo hakan?".


"To wannan yana da nasaba da irin gurɓatacciyar al'ummar da muka yi tarayya da su acikin harkokin mu na yau da kullum".


Kana cikin gida kana jiyo sautin waƙa.


Ka fito ƙofar gida, kana jiyo sautin waƙa.


Ka tafi masallaci, kana jiyo sautin waƙa.


Ka dawo daga masallaci, ka na jiyo sautin waƙa.


Ka tafi kasuwa, kana jiyo sautin waƙa.


Ka dawo daga kasuwa, kana jiyo sautin waƙa.


"Misali, waƙe-waƙe sun ratsa dukkanin lunguna da kowane saƙo, yara da manya kowa yana kunna ta yana sauraren ta fiye da yadda suke sauraren alƙur'ani a rayuwarsu, to kai kana ustazu, ta yaya za ka iya kare kanka daga sauraronta daga garesu? Wannan ba abu ne mai yiwuwa ba".


"Tun farko mun riga da mun bari yahudu da nasara sunci galaba akanmu, sun yaƙe mu har cikin gidajen mu, mun zamto mune muke tayasu daɗa yaƙarmu da kanmu dare da rana, to ta yaya za mu samu zaman lafiya, ta yaya zamu haifar da al'umma tagari bayan yaro ana haifar sa waƙa ce za ta fara dukan kunnensa".


"Za ka samu yaro tun yana ɗan mi-tsi-tsi har ya haddace waƙoƙi masu tarin yawa fiye da yadda ya haddace ayoyin alƙur'ani mai girma, yaro yana cikin tafiya, a maimakon ka ji yana karanta Qur'ani ko hadisi, to yanzu saidai ka ji yana rera waƙa, SubhanAllah! Wannan wace iriyar rayuwa ce muka tsinci kanmu acikinta haka?".


Yaa Allah ka gyara mana zuƙatan mu, kasa mu zamto al'umma bai ɗaya mai ƙoƙarin ɗaukaka addininka da kuma gyara alaƙarsu dakai, Amin.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user