Thursday 2 September 2021

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (38) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga

SANIN MAKAMAN SANA'A


Ba wata sana'a sabuwa da za a gina ta ba tare da sanin makamanta ba sannan ta bayar da abinda ake so in ba sa'a aka ci ba, wasu masu kama sabbin sana'o'i ido rufe dalilin durƙushewarsu ke nan kafin su tsaya da ƙafafunsu, da yawan mutane sukan fara sana'a ne ko su canja daga wata zuwa wata don tana ba su sha'awa ko kuma sun gaji da ta farko ko ba ta basu abinda suke nema, ba wai don sabuwar sun gamsu da sanin makamanta ba.


SANIN MAKAMAN SANA'A


MarubuciBaban Manar Alkasim


Wasu kuma in suka lura ne cewa maƙwabtansu ko wasu nasu da suke yin wata sana'ar suna samun alkhairi sai kawai su yanke cewa su ma ya kamata su jarraba ta, alhali ba a ɗaukar sabuwar sana'a sai an kiyaye bambancin dake tsakanin sana'o'in, tsohuwar sana'ar da kuma sabuwar da za a ɗauka yanzu, mutum ya tambayi kansa: Mai ya sa yake son ya canja sana'a? Ya lura cewa mutanen wurin sun fi buƙatar sabuwan ne? Ko ya ga ana samu ne a cikinta? Kar dai ya kasance ya gaji da tsohuwan ne, ko kuma sabuwar yake sha'awa.


Maganin matsalolin da duk sabon ɗan kasuwa yake fuskanta shi ne sanin makaman sana'a, wannan sanin makaman sana'ar za mu karance shi a bayyane na wasu 'yan kwanaki cikin yardar Allah, kafin sannan mai ya sa nake da sha'awar a ce ina da sana'a? Za ka yi dariya in na ce maka wani ya gaya min cewa sana'ar abokinsa ta fi tasa, da na bincika sai na samu wai 'yammata har faɗa suke yi a kan abokin, kuma duk a dalilin sana'arsa, ni kuwa na taɓa yin sha'awar sana'a don ban son a ce komai sai an ba ni, dukkan mu biyu muna buƙatar ilimi.


Shi wannan sanin makama ya shafi zaɓin sana'ar ne, tsara yadda za a tafiyar da ita sai kuma gudanarwa, galibi irin waɗannan sana'o'i da muke magana sabbin sana'o'i ne, komai jarinka a sabuwar sana'a kai ƙarami ne kana buƙatar sanin makama, koda kuwa kai da kanka kake da sha'awar farawar ko shawara aka ba ka, a ƙarshe dai za a koyar da kai yadda za ka riƙe ta ka kuma haɓɓaka ta tare da duk matsalolin dake kewaye da ita.


Matsalolin su ne: Rashin tabbaci na samun riba tare da kuɗin da za ka narka a ciki a matsayin jari, ko yuwuwar faɗuwa in ba ka samu masu buƙatar kayan ba, wannan in kasuwanci ne, in kuma wata sana'ar hannu ce kamar ɗunki, kanikanci, kafintanci da sauransu, za ka iya jimawa sosai mutane ba su ma san da kai ba bare su ba ka aikinsu, wasu ko askin baba ne in ba su sami wanda suka saba da shi ba gwara su bar kansu haka, kenan duk sana'ar da za ka shiga ba tabbas, kana dai sa rai da samun karɓuwa, sanin makama ya zama dole kenan.


Kalmar da farko na nufin in za ka fara sana'a matuƙar ba wannan sana'ar kake yi ba tuntuni, dole ka sa haƙuri ka nemi gwanancewa a ciki, wace ita ce za ta kawo shuhurar da kake buƙata, in mutum wanzami ne kuma yana yi wa jama'a ƙaho yana ba da magani, sai ya ga ana samu a ƙahon zamani da ake kira "Kofi" ko "Hijama" a Larabce, sai yanke shawarar ya canja kayan sana'an kawai, shi ma dole ya durƙusa wa sanin makamannan, don komai ya koma sabo, dole ya ɗauko daga tushe, suna suka haɗa amma ɗabi'unsu sun bambanta.


1) Kayan aiki: Ƙaho ya bambanta da 'yan kofunan da ake amfani da su a yau, duk da cewa ana ganin jini ɓaro-ɓaro kuma ƙila hakan ya tsoratar da wanda bai taɓa yi ba, sifarsu dai ta bambanta da ƙaho mutum zai fi yarda da su sama da ƙahon, musamman yadda mutum zai iya mallakar nasa na kansa in ya tashi zai tafi da abinsa.


2) Mabuƙata: Irin mutanen da suka saba da ƙahon gargajiya ba su ne za su yi saurin zuwa wurinsa ba, ƙila na zamanin bai yi musu ba, ko kuma ba a saba da shi ba, ko ƙila ya yi musu tsada, dole dai ya koyi aiki da sabbin kofunan ya san kuma irin bayanan da zai riƙa yi wa jama'a na bambancin dake tsakanin ƙaho da kofi?


DUBA WANNANKaranta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (39) Cikin Sauki


3) Wuri: Duk da cewa wanzamai na da wurin zama a wasu ƙauyuka sai dai kuma galibinsu suna yawo ne da zabira, don suna haɗa aski ne da wasu sana'o'in wuri guda, kamar cire belu, kaciya, ba da magunguna da sauransu, yanzu an rarraba waɗannan sana'o'in, wanda zai yi sana'ar ƙahon zamani dole ya ƙawata wurin da zai yi ko don samun mabuƙata, don shi ba kamar wanzami ne da zai riƙa yawo da zabira ba, in ba haka ba ba zai sami mabuƙatan da yake zato ba, shi ma ya dace ya haɗa da magungunan muslunci, don wani maganin zai kawo shi sai ka ba shi shawarar yin kofin don shi ya fi dacewa da shi.


Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user