Monday 25 October 2021

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (39) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga

Sanin makamannan ko dai mu raba shi zuwa gida biyu, ko shi da kansa ya rabu, don akan sami ƙwararre a wani fanni musamman kasuwanci da sana'ar hannu sai mai son koyo ya zauna da shi ya koya ya iya, a ƙarshe ya buɗe nasa shi ma ya samu masu koyon, in kuma ba wannan ba to sai dai makaranta ta tara mutane ta koyar da su, a ƙarshe ɗalibi ya tashi da aniyar koyarwa shi ma, anan ne abincinsa yake, ko in ya yi dace ya shiga sana'ar kai tsaye ya rabu da aikin gwamnati kenan, a taƙaice dai akwai fahimta kala daban-daban game wannan ilimin.


Sanin Makaman Sana'a


MarubuciBaban Manar Alkasim


MANEMIN SANIN MAKAMA


Mai neman sanin makaman sana'a shi ne wanda yake da sha'awa da kuma damar tsayuwa kan wata sana'a sabuwa da yake son farawa, ya manta da duk matsalolin da za su taso masa yayin farawa saboda burinsa na cimma nasara anan gaba, akan fara karkasa irin waɗannan sana'o'i da ake son farawa tun daga 'yan ƙanana da ake farawa a gida har zuwa manyan sana'o'i da ake lissafin jarinsu da biliyoyin nairori waɗanda aka samo su ta hanyar mahalli, wasu sana'o'in na ɗabi'a kamar noma da kiwo ne, sai aikin hannu ko juya jari ta fuskoki daban-daban, duk wanda yake da burin fara wata sana'a ya aza a zuciyarsa cewa farko kenan amma kaza yake so ya zama, to duk aikin da zai yi yana kan hanya ne na ƙoƙarin isa inda yake so, zai yi haƙuri da duk matsalolin da za su riƙa bijiro masa waɗanda an ambato su a baya.


Wato kamar rashin riba a farkon farawa, ko a sayi kayan a maimakon a ci riba sai kuma faɗuwa, in ta juya ma sai karayar jari gaba ɗaya, wanda ɗaya daga cikin waɗannan zai same shi amma ya ci gaba shi ne cikakken mai son cin nasara, in kuma sana'ar hannu ce ya san cewa na farko yana buƙatar ya koyi sana'ar kanta, koda a ce ya iya ta ma to yana da buƙatar sanin cewa nan ne dai wurin da zai fara samun waɗanda suke buƙatar aikinsa, kar ya yi gaggawar son rabuwa da maigidansa, ya bari mutane su san shi, yadda za su bi shi duk inda zai koma ya fara nasa na kansa.


Kenan mun raba lamarin ta fuskar koyon aiki zuwa gida biyu, na farko ya koya har ya gwanance, na biyu ya fara samun mabuƙata waɗanda za su bi shi, anan yaranmu ke faɗuwa jarabawa, don sukan yi gaggawa wurin rabuwa da maigidansu idan suka ga cewa kura ce da shan duka gardi da karɓe kuɗi, tunaninsu kawai su ma fa sun iya aikinnan, ko kuma su ne ma suke yi wani ƙato yana tattara kuɗin hankali kwance, ba su tunanin cewa in fa suka iya aikin mabuƙata suka san su to bin su za su yi, sun kwashe masa mabuƙata, kamata ya yi mai gidansu ne zai yi ƙoƙarin rabuwa da su kafin a fahimci gwanancewarsu abin haushi sai ka ga su da kansu suke neman a yaye su, wannan kam kuskure ne babba.


KASAFIN SANIN MAKAMA


1) SANIN MAKAMAN ƘANANAN SANA'O'I


Galibin waɗannan sana'o'in ko a cikin gida za a yi wasu da dama, kamar: Gyaran gashi, kitso, kayan shago, kamisho, mashawarta kan makarantu da sana'o'i, kafinta, haɗa ruwa, haɗa wutar lantarki, ƙira, kanikanci da sauransu, masu waɗannan sana'o'i za su iya gudanar da sana'o'insu da kansu, ko su sanya wani makusancinsu ya riƙa taimaka musu, ko su ɗauki wani su biya shi. Ɗan kudin da suke da shi, ko rance da wani makusanci zai ba su ya ishe su biyan buƙata, sai ko zuwa rance a banki  ko wani tallafi da gwamnati ke badawa.


2) MATSAKAITAN SANA'O'I


Sana'o'in da sukan iya ƙetare mahallin da mutum ke ciki zuwa wasu sassa da ɓangaro na gari ko ma garuruwa, kamar noma da kiwo, waɗannan sana'o'in akwai farawa akwai kuma faɗaɗawa, mu ɗauki wasu ƙusurwoyi na Arewacin Nigeria: Kaduna a matsayin  misali inda a ƙananan hukumomin Saminaka, Lere za a sami matashin dake noma tireloli na masara, ko shinkafa a Kura dake Kano, ko wake a Zamfara, ko tumatir a Giwa, ko rake a Maƙarfi, ko citta a Kachia da Jaba da dai sauransu, irin waɗannan masu sana'a gwamnati kan iya ƙarfafa musu gwiwa, ta ba su makama da kayan aiki, don ganin an cimma buri, kayan aikin kan iya zama jari na bunƙasa sana'ar, ba ma noma da kiwo kaɗai ba da ma wasu abubuwan na daban.


Irin waɗannan sana'o'in ba ƙanana ba ne, kuskure ne babba sabon mai kama sana'a ya yi rancen kuɗi ya faɗa su ba tare da cikakken ilimi na makaman sana'a ba, kiwo ko na kifi ne akwai dabarbaru da lokuta da nau'in abinci duk waɗannan sai an koya, to bare kiwon kaji da manyan dabbobi, haka noma ma, ba a zuba kuɗi a ƙasa sai an sami cikakken sanin makaman sana'a, masu noman rani kan karɓi taki su karɓi hayar gona da injinan ruwa, galibi duka bashi ne sai an cire amfani, wanda ya faɗa ido rufe in ba sa'a aka ci ba akwai wahala don gwari ne.


DUBA WANNANKaranta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (40) Cikin Sauki


Da wayauna na san masu sana'ar noman rani waɗanda suke yin lambunan da za a shuka tattasai, attarugu, yalo, tumatur da albasa, ba shikenan ba da sauran kayan gona da ake safaransu, galibi bashin jari ake yi sai an sayar a biya kuɗin, manoman kan sami alheri sosai, su kai Legas da garuruwan Inyamurai su sayar su dawo a motocinsu sabbi da suka sayo, in ta juya musu kuma sai dai su gudu su bar direban da kayan, in ya so in ya dawo a kwashi tsiya, sanin makama zai ba da tasa gudummuwa gwaggwaɓa a wannan sashi, a karanci irin kayan gwarin da yake da shiga a shekarar da kuma inda za a sayar da shi, sannan a lura da ƙasar da za a noma da yawan buhunan takin da za a saya, gami da magungunan feshi, sai kuma waɗanda za su taimaka wa mutum ban ruwa da noma.


Za mu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user