Thursday 13 October 2022

Shawarwarin Da Za Su Sauya Rayuwarka Nan Take

Tura Wannan Zuwa Ga

Ga shawarwari guda shida waɗanda za ka iya farawa yau ɗin nan;


1. KA MALLAKI ZUCIYAR KA TA HANYAR LAƘANTAR IKON TAFIYAR DA TUNANINKA: Ba za ka iya tafiyar da rayuwarka a tsanake ba har sai ka laƙanci yadda kake tunani, kuma ka samu iko akan hakan. Kar ka yi saurin fusata ko yin fushi, ka koyi kwantar da hankalin ka da nutsuwa a lokacin da ranka ya ɓaci ko gabanka na faɗuwa yadda ba za ka yanke shawara ba tare da yin tunani ba.


HANYA MAFI TASIRI WAJEN HORAS DA KANKA
Hoto: Spunout

MarubuciBello Galadanchi


2. KA RIƘE WUTA: Duk wani abu mai daraja yana da wahala, kuma samun nasara a komai da kake tunani na buƙatar aiki tuƙuru da riƙe wuta, wato ka daɗe kana yi. Idan har kana so ka cimma burin ka a rayuwa, to dole sai ka ƙalubalanci duk wani abu da ke ɗauke maka hankali, kuma ka zama mai haƙuri saboda ba za su ƙare ba.


3. KA MAYAR DA HANKALI AKAN BABBAN BURIN KA: Idan burin ka shi ne gina sana’ar da za ta kawo maka biliyoyin naira a shekaru goma, to dole sai ka ƙalubalanci ƙananan buri kamar mallakar sabuwar waya ‘yar yayi, ka tara kuɗin ka ta yadda za ka zama mai amfani da kuɗi a hikimance.


Idan har kana so ka cim ma burin ka kuma ka isa inda kake son zuwa, to sai ka yi watsi da wasu ‘yan ƙananan abubuwa da kake so, ko suke ƙayatar da kai. Akwai mutane da yawa da ke jin daɗin kallon ƙwallon ƙafa a maimakon karanta littafi, saboda haka sai ka tunatar da kanka cewa babban burinka ya fi daraja akan ƙananan abubuwa da ke kawo maka nishaɗi a rayuwa.


4. KA FARA A HANKALI: Duk lokacin da ka yi tunanin cimma babban buri, wani lokacin abun yakan ƙalubalance ka saboda girman shi. Abin da za ka yi shi ne, ka rarraba shi zuwa ‘yan ƙanana, sannan ka ɗauki kowane kashi ɗaya, ka mayar da hankali akan shi. Ka tsara jadawalin lokacin da za ka share wajen cimma shi, sannan ka shata wa kanka wa’adin cimma shi. Wannan zai ba ka duka bayanan da kake buƙata wajen cimma burin ka, sannan zai zama kamar titin da za ka bi domin ganin ka samu nasara.


5. KA KULA DA KANKA: Ka kula da lafiyar jikinka da ƙwaƙwalwar ka. Ka ci abinci mai kyau, ka kiyaye sukari da ruwan sanyi, da yawan zama a waje ɗaya. Ka ringa motsa jiki da addu’a. Wannan zai ƙara wa jikin ka lafiya sannan zuciyar ka za ta samu nutsuwa.


6. KA RINGA TUNANIN ALHERI: Ka yi ƙoƙarin mulkar zuciyar ka, idan ba haka ba, za ta mulke ka. Dole sai ka yarda da kanka, kafin wasu su yarda da kai. Idan kana da fara’a da hasken zuciya, to wannan shi ne gimshiƙin ƙara wa kanka ƙarfin gwiwa a rayuwa da zuciya mai tauri da daraja.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user