Wednesday 16 November 2022

Sirrin Zama Mai Arziki A Dare Daya

Tura Wannan Zuwa Ga

Shi arziki nufin Allah ne, kuma za ka iya yin arziki a cikin dare ɗaya. Tambayar anan ita ce ɗorarren arziki fa? Mun ji labaran mutane da yawa waɗanda suka samu abun duniya mai yawa cikin ‘yan kwanaki ko watanni, amma yanzu ina kuɗaɗen suke? Me yasa wasu suke talaucewa duk arzikinsu, wasu kuma suke yin arziki tun ba su da komai? Saboda haka wannan rubutu, zai mayar da hankali ne akan yadda mai ƙaramin ƙarfi zai gina arzikinsa da kansa, kuma arziki mai ɗorewa. Idan kana so ka yi arziki a cikin shekaru goma, to dole ka ɗaura ɗammara yau ɗin nan ka da sa tushe.


YADDA ZA KA YI ARZIKI
Hoto: Freepik


MarubuciBello Galadanchi


Ga abubuwan da kake buƙata;


1. KA NEMI ILIMI


Ko ta wace hanya kake son samun arzikinka, to dole ka nemi ilimi, kuma ka karanta littattafai dangane da wannan harka. Neman ilimi ya ƙunshi neman mutanen da suke cikin wannan harka su ba ka labarai, shawarwari, tarihi, darussa da hikima. Idan akwai littafan da suka sani masu amfani dangane da wannan harka, to ka tambaye su, su ba ka sunayen su ka nema, ka saya, ka karanta. Duk wanda ka yi magana da shi, da duk littafan da ka karanta, za ka koyi abu ɗaya ko biyu a wannan harka. Kana ƙara samun ilimi a wannan harka, to yiwuwar samun nasararka na ƙaruwa. Kowace harka duk sauƙin ta tana da sirri, da dabaru da hikima, kuma dole sai ka fahimce su kafin ka ƙware. Harkar za ta iya kasancewa noma, ko sufuri, gini ko kuma duk wata sana’a da ke ba ka sha’awa. Wahayin da Manzon Allah (S.A.W) ya fara samu shi ne “Ka yi karatu”. 


2. KA NEMI ƘWAREWA


Akwai mutane da yawa da ke koyon sana’a, sannan da sun fahimta kuma suka fara samun kuɗi, shikenan sai kawai su ci gaba da maimaitawa ba tare da neman ƙwarewa ba. Dole ne ka daure, duk da cewa akwai matsalolin rayuwa iri-iri, ka bunƙasa ƙwarewarka. Misali shi ne, idan tsire kake sayarwa, to da ka samu ɗan benci kana bai wa masu saye suna zama akai suna ci, to shikenan abin da za ka share shekaru kana yi kenan. Amma idan kana son ci-gaba, to sai ka koyi yadda ake sarrafa kaza, da kifi, da indomie, da awara, ba tsire kawai ba, da ma wasu nau’o’in abinci da kayan daɗi. Bencin nan, shi ma a canza shi, a sayo kujeru masu laushi a bai wa kwastomomi. Idan da hali ka saka rumfa, ka samu matashi ya buɗe maka shafin Facebook da WhatsApp. Ka samu mai ɗaukar hoto, ya ɗauki hotunan shagonka da abincinka, a ɗora akan shafin facebook ɗinka da WhatsApp. Duk lokacin da sababbin kwastomomi suka zo, to sai ka ba su adireshin ka na Facebook da WhatsApp domin su kasance tare da kai. Ka ƙarbi lambobin su, bayan kwanaki biyu zuwa uku, ka buga musu ku gaisa. Idan suka zo da yara, ka sayo kayan wasa, ka ba su. Ire-iren waɗannan dabarun na kasuwanci su ne za su saka jama’a suna sha’awarka, da sha’awar kasuwancin ka, suna dawowa. 


3. KA TARA KUƊI  DON KA ZUBA JARI


Hanya mai matuƙar tasiri domin samun arziki shi ne adana a ƙalla naira dubu saba’in da biyar a wata (₦75,000), sannan ka sayi hannayen jari. Idan ka yi haka na shekaru 10, to za ka tara miliyan 9 kenan (₦9,000,000), banda ribar da ka samu a kasuwannin hada-hadar hannayen jari. Abin nufi anan shi ne ko nawa kake samu, kar ka raina. Ka tara komai ƙarancinsu. 


4. KA ZAMA MAI SAUƘIN KAI


Ka yi ƙoƙarin rage kashe-kashen kuɗaɗe, sannan ka tabbatar abin da kake kashewa a wata bai kai rabin kuɗin da kake samu ba. Misali shi ne, idan kana samun dubu ɗari a wata (₦100,000), to abincinka, wajen kwana, tufafi da sauran abubuwan rayuwa kar su ɗara dubu hamsin. Ka ga idan ka yi hakan, a ƙarshen shekaru goma kana da miliyan 6 kenan (₦6,000,000). To ina ga abin da kake samu ya fi haka? Kar ka sayi mota mai tsada, kuma kar ka karɓi bashin banki


Ka sayi ɗan ƙaramin gida, ko ka ƙarbi haya. Gida wajen bacci ne kawai. idan ka rufa idanunka, to babu ruwanka da komai kyawu ko girman gidan. Ba dole sai kana amfani da wayar zamani ba, kar da ka damu da abin da mutane za su ce dangane da yadda kake tafiyar da rayuwar ka. Bayan shekaru goma, su ne za su sha mamaki.


5. KA FARA YAU ƊIN NAN KUMA KAR KA YI SANYI


Idan ka ci gaba da jira, to farawa na kara yin wahala, saboda haka ka fara yau ɗin nan domin cim ma burinka. Kar ka yi fargabar sauya hanya idan ka yi wani abu ba daidai ba. Dole ne ka yi kuskure, amma duk wanda ya samu arziki, to za ka ga cewa ya yi kuskure sosai, amma ya koyi darasi, kuma yana ƙoƙarin gujewa wannan kuskure. Ita hanya mai kyau, sai mai tafiya ne yake gane ta. 


6. KA ROƘI UBANGIJI


Akan hanyar ka ta neman arziki, Allah (S.W.T) Shi ne zai haskaka maka a lokacin da kake cikin duhu, kuma ya kiyaye ka a lokacin da kake cikin haɗari. Dole ne ka bi Shi, domin Ya nuna maka hanya mafi alheri.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user