Tuesday 20 June 2023

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (51) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga

16. Mutum ya tsaya yana ta alhinin abin da ya wuce  ba zai dawo da abin da ya rasa ba, ko ya yi ta jin tsoron kar wannan abin da ya same shi ya sake maimaituwa ba zai ba shi damar ya zama mai sukuni ba sai ma lamarinsa ya ƙara sukurkucewa, yaushe mutum zai tsaya yana ta tsoron shiga wata harka saboda abin da ya faru da shi a baya? Tsoron ba zai sa ya sami abin da yake so ba, sai dai ya yi ta damuwa kan wata asara da ya yi a baya wanda ba zai ƙara masa komai ba, kenan akwai wasu matsaloli guda biyu masu takura mutum a kan hanyarsa ta neman arziki wato nadama da tsoro.


Alhinin abin da ya wuce
Hoto: Please Live


MarubuciBaban Manar Alkasim


Babban abin da zai taimaki mutum shi ne ya maida hankali kawai kan abin da yake nema a gaba, idan asara ce ya yi a baya ba ita zai riƙa tunani ba me ya janyo ta don ya kauce wa faruwarta a gaba, idan tsoron gaba yake to ya maida hankali kan tunanin yadda zai kauce wa faɗawa abin da yake gudu, masana za su iya taimakawa da shawarwari ta wannan sashi, galibi shawarwarinsu kan ba da mafita sosai, don wasu kan ba da shawara kuma su taimaka, a taƙaice kar mutum ya saka kansa a kurkukun jimami da yanke ƙauna, ya yi ƙoƙari ya nemi mafita don samun damar isa ga nasara.


17. Mutane na da saɓani kan ingancin wannan amma likitoci kan bayyana cewa samun cikakken barci na da muhimmiyar rawar da yake takawa wurin ƙara wa mutum lafiya, sun ce aƙalla mutum ya sami sa'o'i 8 yana barci, jikinsa zai samu hutu kamar yadda ƙwaƙwalwarsa za ta huta. Sau tari gajiyar jiya kan hana mutum nishaɗin yau, duk yadda aka ce mutum ba lafiya to fa zancen neman arziki ya ƙare kenan, ƙwayoyin halittar dake cikin ƙwaƙwalwa su ma suna buƙatar hutu sosai don su ba mutum damar da zai yi tunanin hanyoyi daban-daban waɗanda za su kai shi ga nasara.


18. Gudun duk abin da zai cutar da mutum, kamar ƙwayoyin hana barci, ko waɗanda za su saka mutum, haka mutum ya ya yi ƙoƙarin cin abincin da zai ƙara masa lafiya, don da ruwan ciki ake jan na rijiya, kar ya ce ba zai kashe kuɗin da yake ƙoƙarin tarawa ba, wani sa'in idan ba a kashe kuɗi kan abinci mai gina jiki ba, za a kashe sama da haka kan maganin da zai warkar da jikin, duk lokacin da aka ce jiki ba lafiya to fa mutum zai iya kashe duk abin da ya tara don dai ya same ta, a guji mummunan abinci, a riƙa motsa jiki, a ƙaurace wa duk abin da zai rikita ƙwaƙwalwa kamar ƙwayoyi ko tabar wiwi ko hodar iblis, idan ƙwaƙwalwa ta rikice komai tsayawa yake.


19. Kar ka cika son kanka sosai, da gaske ne dukiyar kake nema? Tsaya da kyau ka saka ta a gaba, tunda mun san hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka to ka haɗa da waɗanda za su taimake ka tara ta, amma kafin nan idan ka lura da kyau wasu kan yi kisa su ƙwace dukiya, amma sai manyansu su hana ƙananan, dalilin wannan asirinsu yake tonuwa, don ƙananan ba sa yafiya, wani kuma kan sa ma'aikatansa su ci aiki tuƙuru, amma idan aka sami kudi ba sa waiwayar kowa, shi ya sa ƙananan kan ci alwashin tona asiri, a ƙarshe sai dai ogan ya ga lamarin ya dare masa ya rasa ta ina hakan ta faru.


Idan za ka nemi kuɗi ka zama mai yafiya da kau da kai, ka kuma riƙa kallon ma'aikatanka, ya suke shiga? Ya suke riƙe iyalansu? Wani irin suturu suke sakawa? Ya iyalansu suke? Ka yi ƙoƙarin su sami kwanciyar hankali kamar yadda kai ma kake fata, bisa wannan dalilin za su tsaya ƙyam wajen ganin ci-gaban kamfanin don kana kyautata musu, za su ba shi kariya kuma don su ma akwai abincinsu a ciki yana rage musu matsaloli ba za su bar shi ya lalace ba, idan wani ya ga abin da zai cutar da kai nan da nan zai tona, kuma ya yi tsayin daka wajen ba da tasa gudummuwar har sai ya ga an kawar da matsalar, son kai ba zai taimaki mutum ba.


20. Yi ƙoƙari waɗanda ke zagaye da kai su san muhimmancin samuwarka tare da su, wato su fi kowa fa'idanta da kai, yadda idan wani zai same ka su ne na farkon tsayawa kare ka ba tare da ka nemi taimako ba. Wannan wata hikima ce ta musamman mai matuƙar muhimmancin, koda ma a ce ka yi sakaci ba ka yi hakan ba to ba ka makara ba za ka iya gyarawa. Akwai wani ɗan siyasa da ke ɓangaren jagoranci a siyasar ba ya da maƙwabtansa waɗanda suke mara wa ɓangaren adawa suke ganin ba a yi musu adalci ba a zaɓen da ya gudana.


DUBA NA BAYAKaranta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (50) Cikin Sauki


Gwamnati na sanar da cewa ɓangaren adawar ba su ci nasara ba nan take samari suka faɗa gidansa suka yi masa ƙone-ƙone da ta'adi mai yawa, kamar  dai shi ne ya yi aika-aikar da suke zargi, yanzu abin da ya dace tunda 'yan sanda sun zo shi ne a bi samarin nan duk a cabke, aljihun uban kowa ya yi kuka, amma sai ya sayo abinci buhu-buhu ya raba wa iyayensu, ya ce kar a kama kowa, nan take gabar da ake masa ta koma soyayya, yaran suka zama masa garkuwa. Mai son ya zama mai sukuni ga satar amsa.


Za mu ci-gaba Insha Allah.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user