Wednesday 27 March 2024

Hanyoyi 7 Na Samun Nasarori A Sana'ar Shayi Da Kwai

Tura Wannan Zuwa

Ba Mai Shayi da Ƙwai kaɗai ba, kusan kowace ƙaramar sana’a na fama da ƙalubale wajen tallata kanta, saboda masu sana’o’in ba su san yadda za su banbanta kasuwancin su ba da sauran sana’o’i har su yi fice. Kasuwanci gasa ne, kuma dole sai ka fi kowa hazaƙa da dabara da fahimtar kasuwarka kafin ka fi kowa nasara. Ruwa ba ya tsami banza.


Sana'ar Sayar Da Shayi
Hoto: Munaty Cooking


MarubuciBello Galadanchi


Shin idan wani ya tambaye ka ko mene ne ya banbanta sana’arka da sauran kishiyoyinka:


Ko kana amsa wannan tambaya da ƙarfin gwiwa, inda kake bayyana masa dalilin da yasa ka fi kowa ƙwarewa wajen warware wa kwastomanka matsala?


Ko amsarka na taimakawa mai sauraronka nuna cewa ka fahimci buƙatun kwastomominka?


Ko kana iya bayyana muhimmin dalilin da yasa sana’arka ta fi ta kowa fice a sauƙaƙe?


Duk lokacin da za ka banbance sana’arka da saura, ka tabbatar duk wanda ka gayawa ba zai manta ba, kuma zai yarda da kai. Sirrin wannan hikima shi ne, ka tabbatar ka fahimci buƙatar kwastomanka, kuma ka tabbatar ka fi kowa ƙwarewa da burgewa wajen biya masa buƙata. 


Maganar gaskiya wannan ba abu ne mai sauƙi ba, kuma za ka iya jimawa sosai kana wasa ƙwaƙwalwarka kafin tantance yadda sana’ar ka ta fi ta saura fice. Wani lokacin kuma, saboda kusancin mu da sana’ar mu ne yasa ba ma iya fahimtar abin da ya banbance ta da sauran kishoyiyinta.


Duk da haka, idan za ka iya amsa waɗannan tambayoyin, to kana kan hanyar fahimtar yadda za ka tallata sana’arka, yadda ba kowa ba ne zai iya, kuma wannan shi ne zai iya saka wa ka yi fice.


Me kwastomominka suka fi ƙauna dangane da sana’arka?


Me yasa kwastomomin da suka daɗe tare da kai suke tare da kai har yanzu?


Wanne abu guda ɗaya ne mai daɗi wanda kwastoma ya taɓa gaya maka dangane da yadda kake tafiyar da sana’arka?


Saboda haka akwai hanyoyi da za ka yi amfani wajen zama fitacce a duk garinku ko ma ƙasar ku baki ɗaya.


Ga guda bakwai.


Za mu yi amfani da mai shayi da ƙwai a matsayin misali:


1. KA TACE IRIN KWASTOMAN DA KAKE BUƘATA: Idan ka ƙware wajen biya wa irin kwastoman da ke neman sana’arka buƙata, to za ka fi mayar da hankali wajen fahimta da yin fice wajen warware wa wannan kwastoma matsala. Wannan zai ƙara ƙarfin dangantaka tsakaninka da shi, lamarin da zai ƙara adadin kuɗaɗen shiga. 


Idan shayi da ƙwai kake sayarwa, to sai ka mayar da hankali akan samari da ma’aikata waɗanda su ne suka fi buƙatar sana’arka, ba ƙananan yara ko matan aure ba. Idan ka fahimci buƙatunsu, to za ka iya dai-daita wannan sana’a yadda za ta farantawa samari da ma’aikata rai ta ire-iren abincin da za ka sayar, da ire-iren kayan aikin da za ka yi amfani da su domin su ji kamar a gidan amarya suke.


2. KA MAYAR DA HANKALI SOSAI SOSAI WAJEN KULA DA JIN DAƊIN KWASTOMA: Wannan yana da matuƙar muhimmanci. Ka tabbatar ka zarce bakin ƙoƙarin ka wajen tabbatarwa babu kamar ka a wannan sana’a dangane da farantawa kwastoma rai. Tun daga lokacin da ka haɗu da kwastoma har zuwa rabuwarku, ka kula da shi kamar wani sarki, kuma ka nuna mi shi cewa babu wani kamar shi a duniya.


Wannan rubutu yana tuna mun da wani mai shayi a kwanar Freedom da ke unguwar Sharaɗa a Kano. Duk da cewa ba na iya tuna sunanshi, amma har yanzu ina ganin murmushin su da kazar kazar ɗin shi. Duk lokacin da ya samu dama, yana bugo mun waya mu gaisa.


3. KA WARWARE MATSALA: Ka binciki matsalar da mafi yawancin kwastomominka suke fama da shi sannan ya kasance babu wanda ya fi ka ƙwarewa wajen warware wa. Ka tabbatar ka samo hanoyoyin warware waɗannan matsaloli da sauri tare da sakamako mafi inganci.


Idan shayi da ƙwai kake sayarwa, ka lura da tambayoyin da kwastomomi da yawa suke yi, ta nan za ka gane matsalar dake ci musu tuwo a ƙwarya. Idan ba su da shi, to ka tambaye su ko ta yaya za ka faranta musu rai, da kuma buƙatunsu.


4. KA ƘIRƘIRO WANI SABON ABU: Ka ci-gaba da yunƙurin wajen gani ka biya wa kwastoma buƙata, tare da banbance sana’arka da saura ta hanyar ƙirƙirar duk wani abu da zai ƙarawa sana’arka martaba, daraja da biyawa kwastoma buƙata. Idan sana’arka ba ta da banbanci da sauran kishiyoyinka, to ka gudanar da ita ta wata hanya daban ba irin ta ragowa ba, yadda za ka fi warware wa kwastoma buƙata ta hanya mafi sauƙi da sauri. Idan kai mai shayi ne, to ai kusan duka masu shayi tsarin na su kusan ɗaya ne. Katon teburi ne, da kayan haɗa shayi, da kujerun katako a zagaye da teburin. To me zai hana ka samo kujeru masu laushi, dake ɗauke da ɗan ƙaramin teburi a gefe yadda kowani kwasoma zai ji shi kamar wani sarki? Idan suturar da ragowar masu shayi suke sakawa kusan ɗaya ne, to mai zai hana ka samu sutura mai kyau da ban sha’awa, ko ma ban dariya ka sanya? Abun nufi anan shi ne ka tabbatar ka banbanta yadda duk wanda ya tuna ka, sai ya yi murmushi.


5. KA YI WA KWASTOMA TAYIN DA BA ZAI IYA KAUCEWA BA: Ka zama mai fasaha dangane da yadda kake gabatar da sana’arka, yadda za ka ƙara mata daraja a idanun mutane da har ba za su iya kaucewa ba. Misali za ka iya bayyanawa cewa “idan kwastoma bai ji daɗi ba, to za’a ba shi kuɗaɗensa baki daya”. Idan shayi kake sayarwa, to sai ka yi jimlar kayan abinci kamar shayi, ƙwai, buredi da indomie, ka bada farashi mai armashi idan aka kwatanta da sayen su ɗaya-bayan-ɗaya. Za ka iya yin dabaru da yawa da farashi, yadda kwastoma zai ga darajar kayanka da sana’arka, har ka saka shi ruwan ido.


6. A SANKA A MATSAYIN GWANI A SANA’ARKA: Ya zamanto ka yi suna sosai ta hanyar koyarwa da ilimantarwa dangane da sana’ar da kake yi. Ko shayi kake sayarwa, to ka nuna wa mutane basirarka a wannan ɓangare ta yin rubutu, ko haɗa bidiyo ko sauti inda za ka nuna irin baiwa da kake da shi a wannan sana’a. 


Jama’a za su girmama ka.


7. KA SAWWAƘA WA JAMA’A YI MAKA CINIKI: Ka tabbatar ka gina sana’ar ka yadda kowa zai ji sauƙin aiki da kai. Ka bai wa jama’a lambarka ta waya da WhatsApp. Idan kwastoma ba zai iya zuwa wajen ka shan shayi ba, to haɗa shayin, ka bai wa yaro ya kai masa har gida ko ofis. 


Idan ka zama abun farin ciki a rayuwar kwastomominka, to babu shakka za ka zama fitaccen mai sayar da shayi da ƙwai. 


Allah Ya taimaka.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user