Monday 25 March 2024

Matsalar Naci Ko Izza Ko Ƙarfin Iko Ko Takurawa Ko Tilastawa A Soyayya

Tura Wannan Zuwa

Abin da ake nufi da naci dai shi ne nuna ƙwazo da jajircewar mutum a wajan nema da kuma son ya mallaki abin da yake so.


 MATSALAR NACI KO TILAS A YAYIN NEMAN SOYAYYA
Hoto: Etc


MarubuciNura Nakowa


Za ka iya yin naci akan abubuwa da dama kama a harkar kasuwanci ko aiki da wasu ɓangarorin na neman abin duniya. A irin wannan nacin kakan iya jure samu da rashi ba tare da yanayi ba, kuma koda ka shiga wani hali za ka iya samun tallafi ko sassauci daga wasu wuraren.


Shi kuma Naci A Soyayya ba kamar kowanne irin naci ba ne.


Naci a Soyayya tamkar tilastawa ne. Shi kuma so ba a tilas. Abu ne na yarda da aminci da nutsuwa.


Za ka iya neman soyayyar mutum idan ka yi sa'a a cikin ɗan kankanin lokaci a karɓi soyayyar ka. Wani lokacin kuma sai an ɗan ja lokaci kafin a amshi buƙatar ka. Jinkirin da aka samu kuma ba yana nufin ba a son ka daga farko ba ne sai daga baya aka so ka, a'a, yanayi ne yazo da hakan. Hakanan kuma idan aka yi saurin karɓar soyayyar ka, shi ma ba yana nufin an fi sonka ba ne, yanayin ne dai ya zo da haka.


Da akwai mutanen da idan suka ƙyallara idanu suka hango wanda suke so (musammam maza akan mata) sai sun nace akan sai sun yi soyayya da ita.


Kuskure na farko da suke yi shi ne, ba za su tsaya su yi tunanin, shin, za ta so su ko ba za ta so su ba, kawai su buƙatar su na sai sun yi soyayya da ita shi ne a gaba.


Za ka ga saurayi ya kula budurwa da zummar yana son ta domin ita ma ta so shi amma ta ce da shi a'a ko kuma ta nuna masa alamar cewa ba ta yi ko ba ta da ra'ayin yin soyayya da shi, amma kuma a maimakon ya haƙura ya godewa Allah da ya sauƙaƙa masa wahala, ba tare da an wahalar da shi ba aka nuna masa cewa fa wannan buƙatar da ya zo da ita ba za ta karɓu ba. Sai ka ga ya kasa fahimtar hakan.


A haka zai yi ta ƙoƙarin sai ya burgeta ta kowacce siga domin ya sace zuciyar ta, amma kuma ba zai yi nasara ba saboda ba ta son sa kuma tun da farko ta nuna masa haka.


Wasu sukan janye da wuri idan suka fahimci cewa hanyar ba mai ɓullewa ba ce ko kuma su janye don sun ga an fara musu gashin-ƙuma.


Wasu kuma ba za su haƙura ba, hasali ma, cewa za su yi ko ta halin-ƙaƙa sai an so su. Da haka sai ka ga an fake da bin malamai da bokaye domin a tilastawa zuciyar wadda suke so ba ta son su ta dawo tana son su.


Wasu kuma ba za su kai ga bin bokaye ko malamai ba, amma za su zafafa wajan iyaye da 'yan uwa ko dangin wadda suke so don a shawo kanta domin ta yarda a so ta ko a aureta. Ko kuma ma ka ga idan me dukiya ne, zai kashe ko miliyan nawa ne domin a ba shi aurenta.


To shi irin wannan soyayyar me za a kira shi kenan?


Ko da yake bai cancanci a kira shi da soyayya ba tunda an yi amfani da ƙarfin iko da isa wajan tilastawa zuciya karɓar abin da ba ta so.


Duk wanda ya jefa kansa cikin irin wannan chakwakiyar soyayyar, to, ya yi kuka da kansa.


A soyayya ana buƙatar amincewar zukata biyu, watau mutum biyu, waɗanda suka yarda cewar za su shiga cikin rayuwar junarsu. Idan aka samu akasin haka, to tabbas, za a zalunci ɗaya daga cikin su.


So ba a samun sa da ƙarfi ko izza, dole sai da lallama. Duk abin da ake so neman shi ake yi ba ƙwato shi ake yi ba. Shi kuma nema sai da hikima da dabara ake cin ribar sa.


Alhamdu lillah. Idan ka ji dadi to ka sanar da wasu.


A ci-gaba da bibiyar mu a ranakun LitininLaraba, da Juma'a domin ganin abin da muka wallafa na soyayya.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user