Thursday 16 May 2024

Kalaman Bankwana Ga Masoyiya

Tura Wannan Zuwa Ga

Ya na ga kamar fuskar ki ta yi wani iri don kawai zan tafi? Ba kya so na tafi ne shalelena?


Bankwana Da Masoyiya
Hoto: The Digital Reader


Ki yi haƙuri na tafi, ai ina cikin zuciyar ki ko? Kuma ma idan na koma gida zan kira ki. Ki saki ran ki kin ji? Ai ba zan bar ki ba. Ina tare da ke.


Ganin kamar za ki yi kukan nan sare min gwiwoyi yake yi. Na ji kamar kar na tafi.


Ni dai ki yi min alƙawarin ba za ki yi kuka ba, za ki kasance cikin farin ciki, kin yi alƙawari? Yawwa Shalelena. Ina son ki.


Sanusi Kabir wanda aka fi sani da Limamin Masoya shi ne wanda ya gabatar da shi, wakilin mu ya fitar da shi a rubuce, ga dukkan wanda yake son ya saurare shi a ainihin yadda yake, zai iya sauke Audio ɗin ta hanyar latsa nan.


Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun zafafan saƙonnin soyayya da kalaman soyayya na saurare da na karantawa.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user