Wednesday 15 May 2024

Kalaman Neman Yafiya Zuwa Ga Masoyiya

Tura Wannan Zuwa Ga

Jiya na ɓata miki ko? A ki yi haƙuri kin ji? Ni kaina sai daga baya na bibiyi abin da na yi mikin, wanda a ƙarshe na gane cewa ko-kaɗan ban kyauta ba.


NEMAN YAFIYAR MASOYIYA
Hoto: VPics

Na san har yanzu zuciyar ki ba ta daina fushi da ni ba ko? Ni kaina abin da ya fi damuna kenan, wato fushin ki a gare ni, ba na so.


Ƙanwata na san ko kaɗan ban kyauta ba amma ki yafe min kin ji? Dan Allah ki yi haƙuri. Ina son ki.


Sanusi Kabir ne ya gabatar da shi, wakilin mu ya fitar da shi a rubuce, ga dukkan wanda yake son ya saurare shi a ainihin yadda yake, zai iya sauke Audio ɗin ta hanyar latsa nan.


Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun zafafan saƙonnin soyayya da kalaman soyayya na saurare da na karantawa.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user