Sunday 30 June 2024

Siffofi 11 Na 'Yan Cima-Zaune Da Na 'Yan Zaman Kashe Wando

Tura Wannan Zuwa Ga

In taƙaita muku, akwai alamomi 11 dake bayyana mutanen da suke zaman kashe wando a rayuwa. 


1. MAI ZAMA A GIDA DUK LOKACIN DA YA SAMU DAMA: Duniyar nan na jiran ka a wajen gidanku, babu wani abu mai tasiri da zai riske ka a gida, dole sai ka fita ka nema da kanka.


Alamomin 'Yan Cima Zaune da na 'Yan Zaman Kashe Wando
Hoto: Medium


MarubuciBello Galadanchi

 

2. KALMAR DA KA FI ƘAUNA ITA CE “AMMA”: Na yi niyyar zuwa kasuwa amma…. Amma ba haka nake so ba… Amma abubuwa ne suka yi min yawa… Amma za’a samu sauƙi… Amma babu matsala… Amma ba wani abu ba ne. Duk wani mai yawan bada dalilai mutum ne mai kasala. 


3. BACCI YA FI KOMAI: Babu inda kake ƙauna kamar gado, ko kujera, ko tabarmarka. Duk lokacin da ka samu dama, sai ka ce za ka kwanta ka yi bacci. 


4. KOMAI “LAFIYA ƘALAU” NE A RAYUWARKA: Idan ka cika amfani da “lafiya ƙalau” a duk halin da kake ciki, to babu shakka kana da matsala. 


5. KULLUM KANA CIKIN BAƘIN CIKI DA ƘUNCI: Fushi, baƙin ciki, takaici, ƙunci da baƙin rai a kodayaushe alamu ne na mutumin da ke ɗauke da tarin matsaloli. 


6. ZAMAN KASHE LOKACI A KOWANNE HALI: Idan aiki ka je, sai ka yi ta ɓata lokaci kamar kana wani abin arziki, alhali babu wani abin kirki da kake yi. Idan ka dawo gida ma haka, ba tare da bai wa rayuwarka ta duniya daraja ba har sai ka girma ka tsofe. 


7. BA KA DA ABUN YI A KOWANNE LOKACI: Duk lokacin da aka tambaye ka ko me kake yi, sai ka ce “sai a hankali, babu abin da nake yi. Garin ne babu aikin yi”. Babu wanda ya san abin da zai same ka idan ka rasa “yanar gizo-gizo” ko wayar hannu. 


8. KANA ZAMAN JIRAN DAMA DA SA’A: Ba ka neman abokanka saboda ba ka shirya komai ba, kuma ba ka da abun yi. Ba ka neman ilimi saboda kana fargabar samun kanka a yanayin da ba ka saba ba. 


9. BABU WANDA YAKE SON HULƊA DA KAI: Babu wanda yake son hulɗa da mutumin da ba shi da alƙibla. Idan ɓata lokacinka kake yi a zaman duniya, to abokanka da iyayenka, da ‘yan uwanka za su ankara, sannan za su guje ka, saboda kar ka ja su ƙasa tare da kai. 


10. BABU CANJI: Kowace shekara kana kan abu ɗaya, duk lokacin da aka tambaye ka ko me kake yi a ci-gaban rayuwarka, amsar ka guda ɗaya ce, har yanzu ka kasa cimma abu ɗaya, kuma haka za ka share shekara da shekaru. 


11. RASHIN IMANI DA IBADA: Ba ka Sallah balle karatun Al Qur’ani. Ka gagara kammala ilimin boko bare na addini. 


Wato shi Ɗan Adam tara yake bai cika goma ba. Idan akwai alama guda ɗaya da ta shafe ka, to sai ka tashi a tsaye ka fara gyara.


Zaman duniya yaƙi ne, dole sai mun jajirce yau da kullum sannan za mu cimma nasarar rayuwa da ci-gaba mai albarka. 

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user