Tuesday 2 July 2024

Fahimtar Kimar Rayuwa

Tura Wannan Zuwa Ga

Da a ce mun fahimci ƙimar rayuwa, mun kuma fahimci ma'anar mutuwa da abin da ke bayan ta, lallai da mun kame daga munana wa junan mu, kuma da mun zage damtse wajen cika rayuwar mu da rayuwar wasun mu da farin ciki.


Ƙimar Rayuwa
Hoto: Pixabay


MarubuciIbrahim Nuhu Imam Rimi


Idan ka ga mutane sun guje ka a lokacin ƙunci, to ka sani cewa Allah ne ke nufin jiɓintar lamuran ka shi ya sa bai bar ka da wanin sa ba, domin a sanda aka guje ka za ka koyi darussa da dama da za su zamo maka haske cikin abin da ka wuto da kuma wanda kake dosa na rayuwa a gaba.


Ya Allah kar ka yaga mana rigar suturar da kai mana, Kar ka ƙasƙanta mu da tarin aibobin mu, Kar ka yaye mana tsiraicin mu, Ka rufa mana asirin mu duniya da lahira Amin.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user