Monday 1 July 2024

Karanta Cikakken Tarihin Ƙasar Ingila A Yau Da Jiya

Tura Wannan Zuwa Ga

Ingila ƙasa ce da ke cikin ƙasar Ingila. Tana da iyakokin ƙasa da Wales zuwa yamma da Scotland zuwa arewa. Tekun Irish yana arewa maso yammacin Ingila da Tekun Celtic zuwa kudu maso yamma. An raba Ingila daga nahiyar Turai ta Tekun Arewa zuwa gabas da tashar Ingilishi zuwa kudu.


Tarihin Turawan Ingila. (England)
Hoto: CntravellerMarubuciSaliadeen Sicey


Ingila ko UK  ɗaya ne?


Birtaniya, kamar yadda ake kira, ƙasa ce mai cin gashin kanta wacce ta ƙunshi ƙasashe guda huɗu: Ingila, Scotland, Wales da Ireland ta Arewa . A cikin Burtaniya, Majalisa tana da 'yancin kai, amma kowace ƙasa tana da Kayyadadden 'yancin kai.


Jihohi nawa Ingila take dasu?


Ingila Bata Da Jihohi sai dai an raba Ingila gaba ɗaya zuwa gundumomi 48.


Kasashe nawa Ingila ta yi mulkin mallaka?


Daular Burtaniya ta mallaki kashi 23% na al'ummar Duniya. Mulkin Burtaniya ya haɗa da ƙasashe sama da 80 a duniya, waɗanda wasu daga cikinsu ba al'umma ba ne amma sun shiga cikin su. Ƙasashe 56 daga cikin waɗancan ƙasashe sun kasance a cikin Commonwealth.


Garuruwa nawa ne a Ingila?


Akwai birane 51 da garuruwa 935 a Ingila. Wasu manyan biranen sun haɗa da Manchester, Birmingham da Liverpool.


Turawan Ingila sun yi mafari ne daga wata ƙabilar Jamusawa da suka yi hijira daga yankin tekun Baltic zuwa ƙasar Ingila ta yanzu.


Ingila dai ta sami sunan ta ne daga tsohon harshen Ingilishi, wadda a zamanin aka fi sani da „Englaland“ , ma'ana ƙasa mai gaɓobi. Su kuma a al'ummar ƙasar a zamanin an fi sanin su ne da sunan “Anglais”, wato wata ƙabilar Jamusawa da suka yi hijira zuwa Birtaniya, a cikin ƙarni na biyar da ƙarni na shidda.  Su dai waɗannan ƙabilar Jamusawa na Anglais, sun yi asali ne daga zirin kwazazzaɓan Angel dake gaɓar Kil a yankin tekun Baltic. An sami shaidar cewa ɗan adam ya zo ƙasar da muka fi sani a yanzu Ingila ne, tun kamar shekaru 78,000 da suka shige. Masana fasahar tarihin bani adama, sun haƙo ƙasusuwan mutanen da aka binne a ƙasar tun kaman shekaru 5000 waɗanda suka shige.


To amma sai shekaru 6000 da suka shige ne mutane suka fara kafa garuruwa a ƙasar ta Ingila. Ingila dai ta zama haɗaɗaɗɗiyar ƙasa ce mai al'adun ta, da tsarin mulkin ta da kuma harshen Ingilishi, shekaru 927 bayan haihuwar annabi Isa allaihissalam, wato a ƙarni na 15.


Ƙasashen da Ingila ta yi iyaka da su


Ƙasar da a yanzu muka fi sani da Ingila, tana da iyaka ne daga arewa da ƙasar Scotland, daga yamma kuma da ƙasar Wales da kogin Ireland daga arewa maso yamma da kuma kogin Celtic daga kudu.


Ƙasar Ingila ta mamaye yawancin kudu da tsakiyar tsibirin Burtaniya ne a arewacin tekun Atlantica haka kuma Ingila tana haɗa da ƙananan tsibirai su sama da 100 kamar dai tsibirin Silly da kuma Ile of White, ya zuwa shekarar 1284 Ingila‚ 'yantacciyar ƙasa ce har zuwa 1700 inda a ranar ɗaya ga watar Mayu a shekarar 1707, sarakunan daular Burtaniya suka cimma yarjejeniyar haɗewa domin kafa haɗaɗɗiyar daular sarakunan Burtaniya wadda za ta ƙulla ƙawance tsakanin ƙasashen Ingila, Wales da kuma Scotland. A shekarar 1800 ƙasashen guda uku da suka haɗa daular Burtaniya ɗin suka ƙulla wata sabuwar yarjejeniyar ƙawance ta daban da ƙasar Ireland, inda jimla suka zama haɗɗɗiyar daular sarakunan Burtaniya da Ireland 🇮🇪 (United Kingdom 🇬🇧).


Dalilan darewar Birtaniya gida biyu


To amma a shekara 1922 sai ƙasar Ireland ta ɓalle daga yarjejeniyar gammayyar daga sauran ƙasashen guda uku, ta kafa ‘yantacciyar ƙasar Jamhuriyar Ireland. A shekarar1927 kuma, sai wasu gundumomi guda shida da ke cikin ƙasar Ireland, suka ɓalle suka rattaɓa yarjejeniyar zama ƙarƙashin harɗaɗɗiyar daular sarakunan Burtaniya da a yanzu aka fi sani da haɗaɗɗiyar daular sarakunan Burtaniya da Ireland ta Arewa.


Dangantakar yarjejeniyar haɗewa tsakanin ƙasashen guda huɗu, ƙarƙashin daula guda, ta bai wa kowacce daga cikin su, 'yancin gudanar da harkokin su na mulki da kuma gwamnatin su, sai dai kawai akwai gwamnatin tarayya ta‚ 'yan majalisar dokoki, waɗanda za su zauna a babbar majalisar ƙasa, da ta haɗa wakilai daga dukkan ƙasashen huɗu, wato Ingila, Wales, Scotland da Ireland ta Arewa. Tare da gwamnati ƙarƙashin Firayiminista, wanda ke da mazaunin sa a Helkwatar sa ta ƙasa da ke birnin London. Sai kuma sarauniya ko sarkin da ke kan karagar mulki a matsayin shugaban ƙasa.


To har kawo yanzu dai, birnin London shi ne Helkwatan daular, kuma bisa ƙidayar al'ummar ta shekarar 2001, an ƙiyasta cewa, Ingila tana da al'umma kusan kashi 84 daga cikin 100 na dukkan al'ummar da ke haɗaɗɗiyar daular.


Yanzu Dai Ƙasar Ingila Tana Da Yawan jama'a: miliyan 55.98 A Lissafin Shekarar (2018).

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user