Sunday 7 July 2024

Karanta Saƙon Soyayya Na Farko A Soyayya

Tura Wannan Zuwa Ga

Saƙon farko da za ka fara turawa budurwa idan ka gan ta ka ji kana son ta.


Saƙon Soyayya Na Farko A Soyayya
Hoto: Pinterest

MarubuciImran Musa Jahun


Ga saƙon nan a taƙaice..:


Assalamu Alaiki So da ƙauna su ne maƙasudin wannan saƙon nawa, matuƙar zan samu so na ya shiga cikin zuciyarki zan yi farin ciki, zan yi matuƙar farin ciki mara misaltuwa tare da bada jinina da ƙarfina kai har da rayuwa matuƙar kin yarda mu sha ruwan soyayya a ƙwarya guda.


Ba na shakka ko fargaba kamar yadda na fuskanci halayyar ki sun dace da rayuwata da rayuwar masoya a ko'ina take a faɗin duniya, domin ga duk namijin da ya same ki a matsayin mata ya tsira daga wulaƙanci irin na 'yan matan zamani.


Na san za ki yi matuƙar mamakin wannan saƙon nawa, sirrin da ke cikin zuciyata ne, domin zuciyata ta daɗe tana son ki.


Rayuwata ta daɗe  tana ƙaunarki, raina ya daɗe da yabawa da halinki.


Idona ya yaba da suffar ki, bakina kuma a kodayaushe zancen ki yake yi.


Na kamu da son ki kuma so ba na wasa ba, kuma ina buri da zumuɗi da shauƙi idan kika amince da ni a matsayin masoyinki.


Ina son ki. Ina ƙaunarki, kuma an ce dai garin masoyi ba ya nisa a duk inda abun son sa yake, kuma ni a tunanina duk wanda ya ce yana son ka a rayuwa ya gama maka komai na duniya, domin shi so sinadari ne kuma bai taɓa kafuwa ko ɗoruwa sai da jinsi guda biyu. Ina mutukar ƙaunarki a raina, tun daga lokacin da na fara tozali da kyakkyawar fuskarki a gare ni, da fatan za ki amshi batuna.


Sai na ji amsata daga gare ki nan bada jimawa ba, na gode ki huta lafiya.


Daga mai ƙaunarki a kowanne irin hali Imran.


Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun zafafan saƙonnin soyayya da kalaman soyayya na saurare da na karantawa.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user