Sunday 7 July 2024

Karanta Hikayar Wani Falke Da Baƙo

Tura Wannan Zuwa Ga

Wani falke ne yake cin kasuwar wani gari mai nisan tafiyar kwana goma sha biyar daga garinsu.


Hikayar Wani Falke Da Baƙo
Hoto: Down


MarubuciSadiq Tukur Gwarzo


Shi wannan falken sana'arsa ita ce sayar da auduga. To duk sa'ar da ya zo wannan garin sai ya sauka a gidan wani mutum wanda suka saba.


Saboda irin sakayyar da falken nan ke yi wa mai masaukinsa, idan kasuwa ta watse, sai ya zama ba shi ba ma har jakunansa ba su rasa abin taunawa.


Wata rana sai falken nan ya zo, suna hira da mai masaukinsa a zaure, sai ga wani mutum ya zo daga shi sai lagensa, ya ce yana neman masauki. 


Falke da mai masaukinsa suka riƙa yi wa mutumin nan kallon uku kwabo. Kai daga ƙarshe falken nan ya ce shi bai amince a bai wa wannan masauki ba don ba su san ko wane iri ne shi ba.


Da mutumi ya ji haka sai ya ce, "Don kun gan ni cikin wannan kama shi ya sa za ku wulakanta ni? To ai ni ma mai gidan kaina ne yanzu ma shanu na kai kurmi na sayar. Tafiya ce ta mayar da ni haka".


Sai ya ɗaga hammatarsa ya jawo wani burgami ya ce, "Ni ma ga tawa dukiyar, mai irin wannnan kuwa me zai tsaye tsiwace-tsiwacen dukiyar wani."


Ya zazzage jakarsa suka ga kuɗi irin wanda ba su taɓa gani ba. Nan da nan hankalin falke ya tashi, sai zare ido yake yana lasar baki. Mai gida kuwa sai ya ce da mutumin nan, "don Allah ka yafe mu. Ka san halin duniyar tamu mutumin yau abin tsoro ne."


Falke kuma sai ya ce "Shi kenan a yi masa masauki tare da ni, ka ga na huta da kwana ni ɗaya".


Da baƙon nan ya ga masaukinsa sai ya ce to zai isa kasuwa domin kuwa gobe ranar kasuwa. 


Ya kama hanya ya tafi. Yana isa kasuwa sai ya sami wani lungu ya cire kuɗinsa daga cikin burgami ya cuccusa su cikin bantensa ya sayi daƙuwa ya cusa cikin burgamin kamar ba a cire kome daga cikinsa ba.


Baƙo ya kama hanya ya koma masauki.


Da dare ya yi aka zauna ana hira sai farken nan ya yi shimfiɗa ƙasa da inda jakar mutumin nan take rataye.


Ana cikin hira sai ya yi hamma, ya yi miƙa da wayo ya miƙe hannunsa ya taɓo jakar nan ya ji har yanzu kuɗin na nan. Da an ɗan jima duk sai ya yi haka.


Can sai ruwan sama ya ɓarke kamar da bakin kwarya, sai baƙon nan ya lunsashe idanunsa ya shiga minsharin ƙarya kamar ya yi bacci.


Da farken nan ya ji gari ya yi tsit sai ya zabura ya figi burgamin nan taf da daƙuwa ya auna da gudu daga shi sai gajeren wando ga shi ana ruwa.


Da baƙo ya ga haka sai ya tashi sannu ya tafi ya tayar da mai gidan ya ce masa "Ka ji abin da mutumin nan ya yi mini".


Gari na wayewa sai mai gidan ya ɗauki baƙon nan suka tafi suka shaida wa sarkin garin abin da ya faru. Sarki ya sa aka kama jakunan falke da kayan audugarsa aka sayar aka ba baƙon nan aka ce ya ci da haƙuri Allah ya saka masa.


Baƙo kuwa sai ya raba kuɗin nan biyu ya ba mai masukinsa rabi, rabi kuwa ya tara almajirai da nakasassu ya yi ta sadaka.


Ya bar garin ana ta yi masa addu 'ar Allah ya kiyaye gaba.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user