Saturday 6 July 2024

Karanta Hakikanin Tarihin Rayuwar Annabi Idris (A.S)

Tura Wannan Zuwa Ga

'Idris ( Da Larabci: إدريس) tsohon annabi ne da aka ambata a cikin Alkur'ani, wanda Musulmi suka yi imani da cewa shi ne Annabi na uku bayan Seth. Shi ne annabi na biyu da aka ambata a cikin Alkur'ani.


Tarihin Annabi Idris  (A.S)
Hoto: Iqna


MarubuciSaliadeen SiceyWane ne Annabi Idris?


Idris ya kasance mutumin kirki mai faffaɗar ƙirji yana magana da murya ƙasa-ƙasa. Ana kuma cewa dogo ne kuma kyakkyawa kuma kodayaushe yana magana cikin nutsuwa. Annabi Idris ya kasance mai matuƙar sha’awar sani, yana yin tunani a kan fa’idar duniya da mahaliccinsa ya yi  daga sama, da ƙasa, da wata, da taurari da gajimare. 


Idris bawan Allah ne na gaskiya, don haka ne Allah ya zaɓe shi a matsayin Annabi kuma Manzo, kuma ya zaɓe shi a matsayin shugaba a kan ‘ya’yan Adam.


Abin da ya fara bayan mutuwar Shiat shi ne mutanen Kayinu sun rasa jagora kuma zunubi da ɓarna sun fara ƙaruwa da sauri kuma suna yaɗuwa. Idris ya kasa jurewa kallon mutanensa suna faɗawa tarkon Shaiɗan. Don haka Allah ya umurci Annabi Idris ya yi kira da a yi jihadi (yaƙi mai tsarki) a kan gurɓatattun mabiya Qabil (Kain) — Idris shi ne Annabi da Manzo na farko a tarihin Musulunci da ya yi Jihadi da fasadi.


Kuma kamar yadda Allah ya umarce shi, Idris ya tara rundunar mutane ya yi yaƙi da sunan Allah a kan azzalumai, suka yi nasara.


Me aka san Annabi Idris da shi?


Anuhu shi ne annabi Idris. Shi ne na farko a cikin ’ya’yan Adamu da aka ba annabta kuma shi ne  ya fara rubutu da alƙalami.


An siffanta shi a cikin Alkur’ani a matsayin “amintaccen” kuma mai “haƙuri” sannan kuma Alkur’ani ya ce an ɗaukaka shi zuwa ga matsayi babba.


ALLAH SUBHANAHU WA TA ALA YANA CEWA


وذكر في الكتاب إدريس إنه كان صدقاً نبينا ورفعناه مكا نا عليا


KUMA KA AMBACI ANNABI IDRIS (ALAIHISSALAM) A CIKIN LITTAFI HAƘIƘA SHI ANNABI NE MAI YAWAN GASGATAWA, KUMA MUKA ƊAUKAKA SHI A GURI MAƊAUKAKI.


Annabi IDRIS ALAIHISSALAM sunan sa na asali wanda aka yanka masa rago dashi shi ne, AKHNUKH, ɗan Yardu ɗan Mahala'ilu, ɗan Kainanu, ɗan Anushu, ɗan Shisu, ɗan Annabi Adam Alaihissalam.


Sannan an ambace shi ne da suna IDRIS sabo da yawan karatun littattafai da yake yi, kuma shi ne wanda ya fara fiƙe alƙalami, kuma shi ne wanda ya fara rubutu, kuma shi ne wanda ya fara rubuta littattafai wato (TA'ALIFI).


Kuma shi ne farkon wanda ya fara bincike a cikin ilimin taurari, da na lissafi, kuma shi ne ya fara ɗinki a duniya wato (sana'ar Tela) domin su mutanen wannan lokacin bargo ko mayafi suke yafawa,.


A lokacin da Annabi IDRIS ya bayyana sai ya sami zare da allura ya ɗinka riga ya saka, da mutane suka gani sai wannan riga ta ba su sha'awa, sai suka dinga kawo masa mayafan su da bargunan su yana maida musu su riga, domin a lokacin babu wanda ya iya ɗinka riga sai shi a duniya, sannan sai daga baya mutane suka dinga kwaikwayon sa, sannan shi ne wanda ya fara ƙera sikeli, wato ma'auni.


Kuma baya cin wani abu sai da kuɗin da ya samu na wajan sana'arsa, ita ce ɗinki, (tela) Amma duk da wannan sana'ar ta Annabi Idris ba ta hana shi zikirin Allah ba, hasali ma, duk lokacin da zai soka allura sai ya ambaci sunan Allah haka nan idan zai zare ta, sannan idan wani abu ya shagaltar dashi bai ambaci Allah ba, a sa wata allurar to fa sai ya warware wannan ɗinkin gaba ɗaya, ya sake wani wanda zai ambaci sunan Allah gaba ɗaya a cikin yin ɗinkin.


اللهم صل وسلم وبارك على سيدنا ونبينا وحبيبنا محمد وعلى آله وصحبه أجمعين وسلم تسليما كثيرا إلى يوم الدين


ALLAH SUBHANAHU WA TA ALA ya saukarwa Annabi IDRIS ALAIHISSALAM abun karantawa guda 30.


A lokacin da aka aiko shi ya zama manzo, sai Annabi IDRIS ya shagala da karanta wannan littafai, babu dare babu rana, mafi yawa daga cikin lokacin sa, sabo da yawan karatun waɗannan littattafai ne da yake yi, sai mutanen sa suka sa masa suna IDRIS ma'ana (mai yawan karatu) sannan da wannan suna ne Ubangiji maɗaukakin sarki ya ambace shi a cikin Alkur'ani mai girma.


Sannan Ubangiji ya aiko Annabi IDRIS zuwa ga ƴaƴan Ƙabilar ɗaya daga cikin ɗan Annabi Adam Alaihissalam wanda ya kafurta suka zama suna bautawa gumakan nan guda 5 wanda Ubangiji Subhanahu wa ta ala, ya ambace su a cikin Kur'ani mai girma, su ne;


Wudda, Da Yagusu, da Ya'uƙa, da Nasara, da Suwa'a, haka nan Annabi IDRIS ALAIHISSALAM ya dinga kiran su izuwa bautar Ubangiji Subhanahu wa ta ala shi kaɗai ba tare da sun haɗa shi da kowa ba.


اللهم صل وسلم وبارك على سيدنا ونبينا وحبيبنا محمد وعلى آله وصحبه أجمعين وسلم تسليما كثيرا إلى يوم الدين


Malam Ibn Ishaq ya ruwaito cewa shi ne mutum na farko da ya fara rubutu da alƙalami kuma an haife shi ne a lokacin da Annabi Adamu ya cika shekaru 308 a rayuwarsa. A cikin tafsirinsa aya ta 19:56-57, malamin tafsirin Ibn Kathir ya ruwaito cewa: “A cikin Tafiyar Dare, Annabi (SAW) ya wuce shi a sama ta huɗu."


Alƙur'ani 


An ambaci Idris sau biyu a cikin Alkur’ani, inda aka bayyana shi a matsayin mutum mai hikima. A cikin sura ta 19 a cikin Alkur’ani, suratu Maryam, Allah yana cewa:


Kuma ka ambaci Idrĩs a cikin Littãfi cewa: Ya kasance mai gaskatãwa, kuma Annabi, kuma Muka ɗaukaka shi zuwa ga wani wuri maɗaukaki.


Daga baya, a cikin suratu ta 21, al-Anbiya , an sake yabon Idris:


Kuma (ka ambaci) Ismã'ĩla da Idrĩsa da Zul-kifli , 19 dukansu (maza) mãsu haƙuri.


Kuma Muka shigar da su a cikin rahamar Mu, kuma sun kasance daga sãlihai.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user