Wednesday 18 September 2024

Karanta Gajeren Sakon Soyayya Na SMS Ga Masoyiya

Tura Wannan Zuwa Ga

Sau da dama na kan yi mafarkin mun yi aure, na zama sarki kin zama sarauniya mai juya akalar gidanmu na aure, muna rayuwa irin ta farin ciki wadda kowanne masoyi ke buri da nufin aiwatarwa a zuciyarsa, sai dai kash a irin wannan yanayi ne nake farkawa sannan na gane mafarki nake ba gaske ba.


Gajeren Sakon Soyayya Na SMS Ga Masoyiya
Hoto: Depositphotos

Marubuci:- It'z Nazeephancy DH


Masoyiya, ina fatan watarana mafarkin nan ya zamto gaske. Na yi alƙawarin cika zuciyarki da farin ciki.


Ba shakka ina sonki.


Koda kuwa so cuta ne kamar yadda mutane suke faɗa, na yarda na rayu na mutu a cikin irin wannan cutar, domin kuwa na kamu ta kowanne ɓangare da cutar son ki na tabbata ba zan warke ba har ranar mutuwa ta.


Don Allah ki so ni kamar yadda nake son ki don Allah, tabbas ina ƙaunarki masoyiya.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user