Wednesday 18 September 2024

Wakar Ina Nazari A Rubuce Ta Hamisu Breaker

Tura Wannan Zuwa Ga

Aaaa yii! Ina nazari, ni fa kamar so yai mini illa.


Ki lura da ni, ko zan warke wataƙila.


Ke ce sanadi wasu ke mini kallan gaula.


Suke zunɗena, ni kuma ban iya ce musu ƙala.


Ban san ki tafi.


Waƙar Ina Nazari A Rubuce
Hoto: HB Records


Ni ban san ki mini bankwana.


Ya ɗan ka ɗafi, so naki ya kama maganaina.


Ya hana ni, sukuni kar ki bari a ji kukana.


Ki yarda da ni.


Ki rufa ni.


Ki saya asiraina.


Komai kika ce ni ba zan ƙi na amshi buƙatu ba.


Ba zan iya cutar da ke in yi wa kaina ba.


Ni ban ga abin da za ki min ba zan haƙure ba.


Ki so ni kawai na ba ki dama ban janye ba.


Yarda da masoyi.


Yarda tushen ƙauna.


Ki gane ina yi.


So naki na damuna.


Ban gane sanyi, kuma ni ban gane zafi.


Ban gane kaina.


Dafin so ke mini zafi.


Ina ta bilayi.


Jikina yau ba ƙarfi.


Abin da nake ji, in za na kwatanta ya fi.


Ki tarbe ni.


Kin ga inai miki so bisa gaskiya.


Ki kalle ni.


Kin ga wasiƙa ce buɗaɗɗiya.


Ki same ni, za ki ji tsantsar sirrin zuciya.


Kika karɓe ni.


Kwa to ƙauna ta zauna lafiya.


Ki yi mini rumfa na fake a gari nasu ƙauna.


Yadda kike so na tsaya ko kuma na tsugunna.


Ki daina tunanin ni ma zan yaudari kaina.


Ba zan saɓa miki ba, in kin zama mai ɗakina.


Kawai mu yi soyayya.


Kuma kar mu yi jayayya.


A kai naki na shirya.


Kuma ba na ja baya.


Ina da farar aniya.


Farar aniya laya.


Ki nai mini alkunya.


Irin na masoya.


Hamisu Breaker ne ya rera wannan waƙar, wakilin mu kuma ya fitar muku da baitocin ta a rubuce don jin daɗi  ku. Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kullum don ci gaba da samun zafafan waƙoƙi a rubuce.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user