Saturday 26 October 2024

Shin A Zahiri Akwai So Ko Duk Ƙarya Ce?

Tura Wannan Zuwa Ga

In dai akwai wani abu wai shi dangi na so, to ina son yake, kuma yaya yake? Ni dai ra'ayina tuni na fidda a fili domin kuwa ni a tawa fahimtar ba wani abu wai shi so, Malumfashi (1988).


Shin so da soyayya na ƙulluwa ne a lokacin da aka yi aure?
Hoto: About Islam

Marubuci:- Ibrahim Malumfashi


Sai dai kar ka ɗauka na ci kubeji a wannan ra'ayi nawa, domin kuwa masanin Falsafar nan Schopenhaber kamar yadda ya yi bayani a cikin Encyclopedia of Philosophy, yana mai ganin cewa ba wani abu wai shi so a tsakanin mutane, sai dai a tsakanin mutum da mahalicci. Wannan ne ya sa yake faɗar cewa, mawaƙa da marubuta Larabci na ɓata lokacin su ne kawai wajen rubutu, domin kuwa abin da suke ma laƙabi da so, ba so ba ne, sai zagi, cin mutunci, batunci/ɓatanci, kisa da sauran munanan al'amura, wanda kamar yadda ya bayyana, hakan na faruwa ne saboda mawaƙa da marubuta sun maido so a matsayin saduwa a tsakanin mace da namiji.

 

Na san za a so a san dalilin da ya sa na ɗau wannan tsattsauran matsayi, to kada mu nemi kai ruwa rana. In dai so shi ne ƙawa-zuci a tsakanin mutane da abubuwa, to me ya sa a kullum na dubi rayuwarmu ta yau da kullum sai yawan yaji mata ke yi, sai tashin hankali a tsakanin ma'aura? Shin me ya sa, yawancin waɗanda ake ce wa masoya, in ka kalle su; sai ka ɗauka aradu ce ta faɗa musu? 

 

In dai akwai so, ta yaya kullum muke ta fama da tsintattun 'ya'ya da uwayensu suka yi watsi da su, bayan haihuwa? Mace nawa muke jin a yau za ta yi da-na-sani dangane da auren mijinta (wanda a da take matuƙar so)? Shin mazaje nawa ne yau za ka ji na faɗar, ai gidan bai shigo, domin kurar nan, na ciki (ita fa ce masoyiyar)? Yau maza nawa ke a asibitin mahaukata, saboda irin kisan mummuken da matansu (masoyansu?) Suka yi musu a gida? Shin nawa ne daga cikin mutane muka ji sun ɓata, saboda so, so fa ne ke sa ai kisa! Na ga wadda mijinta ya watsa mata fetur, alhali kafin su yi aure, ta fi farin wata haske a wajensa. Na ga mai ƙafa ɗaya. Na ga mai fasasshen kai. Na ga mai ido ɗaya. Na ga mai fasassar mota. Na ga mai yagaggar riga. Na ga wadda ta daɓa wa mijinta wuƙar fawa. Na ga wadda ta ƙone mijin ƙurmus. Duk wai saboda me? So!

 

Shi kuwa wannan abu so, zan so in gan shi, don kuwa ko bom ya shafa masa lafiya wajen ɓarna. Wai ma mun manta cewa, karuwa mai neman maza da mace mai maɗigo, da namiji mai neman mata, da namiji mai yin luwaɗi, duk bisa ginin so suke waɗannan abubuwa? Shin mazinaci da mazinaciya, masu aure da marasa aure, shin me ke kai su ga haka, so! Kai lallai da sake game da fahimtar da ake da ita ta so da kuma soyayya. 

 

Kuma lallai in har biyan buƙata ba shi ne so ba, a'a shi dai ne ƙololuwar so, to ina son yake? In an ce taɗi da zance da hira da namiji ke yi da mace kafin su yi aure ko su sadu (ba ta hanyar aure ba), waɗannan matakai na kai wa ga so, to ina son yake? Ni a nawa ɗan guntun tunanin, sai na ga cewa, batun da ake yi na cewa akwai so har iri huɗu: 

 

1. Na so-an-so (Soyayya).

2. Na-so-an-ƙi (Soƙiyayya).

3. Na-ƙi-an-so (Ƙisoyayya).

4. Na-ƙi-an-ki (Ƙiyayya).

 

Waɗannan abubuwa ba su bayyana mana mene ne so ba, in har ka-so-an- so, wato soyayya ta ƙullu, mene ne son, shin dariyar da macen ta yi maka, ko kuwa amsar da ta yi maka hannu bibiyu, ko kuma amsawa da ta yi ni ma ina son ka, shi ne so da soyayya? Me ka so, me ta so, kuma yaya son yake? Shin so shi ne biyan buƙata, kashe zalaƙar zuci, ko kuwa kwanciyar hankali? In dai waɗannan su ne so, to me ke kawo bala'i da tashin hankali a ranar da mutum bai kai ga manufarsa ba? Sai dai in ba daɗi ba ne so, sai dai bala'i. Ni dai har yau biɗa nake ko akwai wanda ya ga so, ya kawo mini shi zan ba shi kyauta, domin kamo mana wannan mugun abu don mu yi gaba da shi daga rayuwarmu.

 

Na faɗi haka ne don ganin cewa ban ga wanda ya sami so ba hankalinsa kwance, ko nata kwance. Shin akwai wanda ya taɓa ganin waɗanda suke soyayya suka kwashe ƙalau? Shin tatsuniyarmu kullum tana wuce ta Laila da Majnun ko Romeo da Jullet? Kai ai nan da sake don ko waɗannan ba soyayya suka yi ba, sai wahalar da kai da hauka.


Manta da waɗancan ma, dawo nan kusa, shin ka taɓa ko kin taɓa tambayar ma'aurata biyu da suka shekara 20 tare, suka faɗa maku/muku cewa ai soyayya ƙalau, in ma da akwai ta? Ƙila wani ya ce ai ba so sai na uwa da ɗanta, ƙila kai a wurinka, ai mahaifiyarka abin so ce abin ƙauna ce, kuma ba wadda kake so irin ta, amma shin ka taɓa tambayar mahaifinka ka ji irin zafin da take ba shi? Don haka ba ni jin cewa lallai akwai so, tatsuniya ce kaɗai, ba batun gaskiya a ciki? 

 

Mu yi tunani bisa wannan batu fa da kyau. Me ke sa mace ta ce wai ta mace wa yaro. Me ke sa yaro ya sami yarinya ya dinga zabga mata ƙarya, ke ce rayuwata, ke ce abin tunanina, ke ce abin ƙaunata, ke ce tauraruwata, ke ce zan so da ƙauna, sai mutuwa ka raba. Ana ɗaura musu auren, tana tarewa, tana haihuwa, sai ka ji ya fara 'yar murya, ni fa amarya zan yo?  

 

Me ya sa mace za ta auri namiji su yi shekara 20 tare, suna ta soyayya, amma ranar da Azara'ilu ya zo ya ɗauke mijin, sai 'yan koke-koke da 'yan murje-murjen ƙarya, bayan 'yan watanni sai ka ji ta sake wani auren? Shin wannan shi ne so da soyayya? Me zai hana ta zauna ba aure har abada tun da shi marayin/ɓarayin rayuwar ya tafi?

 

Shin nawa daga cikinmu (maza) muke turke yarinya muna faɗa mata, ni in ba ke ba sai dai rijiya. In ba ke ba masai. Ni in ban same ki ba, rayuwata ta lalace. A buga, a raya, a kuma yi tattaki bai same ta ɗin ba. Wani can ya aure ta. Amma wannan bawan Allah bai faɗa masan ba, bai faɗa rijiyar ba, bai kashe kansa ba. Can sai ka ji ya faɗa neman wata can daban, idan aka yi sa'a kuma ya same ta, sai ka ji yana faɗar, rashin wance da na yi, ai ɓata lokaci ne kaɗai, idan mata ne ba ga su nan kamar jamfa a Jos ba. Ni kuma na ce ai ka san da su a jamfa a Jos ɗin, amma ka liƙe wa wancan ɗin da ba ka samu ba. Shin so shi ne ƙarya in har akwai shi? Shin wai mene ne so? Ina kuma yake? Yaya kamarsa  take? 

 

Mai sauraro shin me kyarkyarar zakara ke nunawa gare mu? Shin me barbarar taure ke neman fahimtar da mu? Kana jin cewa ba su kama da ƙaryar da namiji ke yi wa mace da zaran ta saki jikinta da shi, gobe sai ka ji ya sake  sheƙa? 

 

Shin so da soyayya na ƙulluwa ne a lokacin da aka yi aure? Shin soyayyar da ba ta kai ga aure ba me za a kira ta? Wahala ko soyayya? Shin mene ne bambanci tsakanin tsarkakakkiya da kuma ɓatacciya? Shin wai don an nemi yarinya an kuma sadu da ita, soyayyar ta ɓaci ke nan? Ana nufin cewa duk irin soyayyar wai da ke nan tsakanin mace da namiji wadda ba ta kai ga aure ba, ita ba soyayya ba ce? Idan haka ne ashe su dabbobi da ƙwari da tsirrai su ba su da so balle soyayya? Don kuwa ba a taɓa ban goro ba aka ce mana an ɗaura aure a tsakanin akuyar gidan Malam Mande da ɗan akuyar gidan Malam Mati.


Ashe mai karatu darbejiyar/dalbijiyar ƙofar gidan Malam Musa na da miji ni ban sani ba. In dai ba su da aure irin wanda muka sani, to mene ne soyayya in akwai ta? A bisa gaskiya zan so na sami bayani game da yadda soyayyar taure, in har akwai ta, take? Ƙila kuma tashi ma soyayyar ta aure ce. In kuwa ta aure ce, shin wace ce matar tasa, mahaifiyarsa? Ƙanwarsa? 'Yarsa ko kuma ɗiyar da ya haifa? Wai shin mene ne so in har akwai shi? Kala yake canzawa kamar hawainiya duk lokacin da ya ji ya gaji da waccen kalar, ko kuma kamar dala yake, tsuntsuwar nan mai ɗauke da launi-launi a jikinta a lokaci guda, in fa akwai shi, ina nan jira ina kuma saurare!

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user